13
Feb
DAGA JOHN D. WADA a Lafiya Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Honorabul Danladi Jatau, ya rantsar da mambobin majalisar biyu wadanda suka lashe zaben cike gurbi wanda aka gudanar a karshen mako da ya gabata a mazabunsu. Mambobin biyu da aka rantsar su ne; Hon. Mohammed Adamu Omadefu (APC Keana) da Hon. Musa Ibrahim Abubakar (NNPP Doma ta Kudu). A jawabinsa a lokacin da yake rantsar da sabbin ‘yan majlisar a zauren majalisar da Lafiya Fadar Gwamnatin jihar, Kakakin Majalisar, Danladi Jatau, bayan ya taya 'yan majalisar murna dangane da sake mallakar kujerunsu a majalisar, ya kuma kalubalence su da…
