20
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a Jam'iyyar PDP ya ce zargin da tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC Chief Bisi Akande ya yi cewa idan PDP ta dawo mulki 'yan Nijeriya za su sake shiga qunci ba gaskiya ba ne. Alhaji Sule Lamido ya ce duk dan APCn da yake ganin PDP ce ta lalata Nijeriya to da shi a ciki, kasancewar shi ma asali dan PDP ne. Sule Lamido ya ce ya yi mamakin kalaman Bisi Akande kan cewa PDP musiba ce, annobar bala'i ce azaba ce, amma duk da hakan…
