Cutar Korona: Abu Dhabi ta haramta tarurrukan shaƙatawa da na bukukuwa

Daga BASHIR ISAH

A matsayin wani mataki na yaƙi da yaɗuwar annobar korona a Abu Dhabi, Kwamitin Kula da Agajin Gaggawa, rikice-rikice da Ibtila’i na Abu Dhabi ya sanya dokar haramta tarurrukan shaƙawata da na bukukuwa a faɗin birnin sai dai ɗan abin da ba za a rasa ba.

Kwamitin ya ce daga ranar 7 ga Fabrairun 2021, an taƙaita adadin mutane da aka amince su halarci taron bikin aure da na zumunta zuwa mutum 10, sannan mutum 20 game da tarurrukan da suka shafi jana’iza da zaman makoke.

Haka nan an taƙaita yawan mutanen da aka yarda su gudanar da harkokin kasuwanci da yawon shaƙatawa, duka dai da zimmar yaƙi da yaɗuwar cutar korona a ƙasar.

Bayanan kwamitin sun nuna cewa an rage yawan mutanen da aka amince su yi hada-hada a manyan shagunan sayayya zuwa kashi 40 cikin 100, sannan zuwa kashi 50 cikin 100 a ɗakunan motsa jiki, wuraren shaƙatawa a bakunan teku masu zaman kansu da wuraren wanka.

Su kuwa ɗakunan cin abinci, shagunan shan shayi, otel-otel, lambunan shaƙatawa da wuraren shaƙatawa a bakunan teku mallakar gwamnati, an rage yawan mutane zuwa kashi 60 cikin 100.

Yayin da aka rage wa taksi-taksi yawan fasinjojinsu zuwa kashi 45 su kuwa bas-bas kashi 75 aka lamunce su rinƙa ɗauka.

Jaridar Khaleej Times ta ruwaito kwamitin na cew zai yi da gaske wajen sanya ido don tabbatar da jama’a sun mutunta wannan sabuwar doka, tare da hukunta duk wanda aka samu da laifin take ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *