Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta tsare tsohon Mataimakin Gwamnan Imo a kurkuku

Daga WAKILINMU

Kotun Majastare mai zamanta a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ta tsare tsohon Mataimakin Gwamnan Imo, Gerald Irona, a gidan yari.

Alƙalin kotun, C.N Ezerioha ne ya ba da umarnin haka yayin zaman kotun a ranar Alhamis.

A ranar Laraba ‘yan sanda suka cafke Irona a gidansa da ke Owerri kafin daga bisani aka gurfana da shi a kotu.

A cewar ‘yan sanda, an kama shi ne saboda furucin tada fitina da ya yi a Kotun Ƙoli yayin da ake shari’a tsakanin Gwamnan Hope Uzodimma da tsohon Gwamna Emeka Ihedioha.