Firaministan Ƙasar Sin ya jaddada buƙatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki

Daga CMG Hausa

Firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya jaddada buƙatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki, da farashin kayayyaki, da samar da guraben ayyukan yi.

Li ya yi tsokacin ne yayin taron majalissar gudanarwar ƙasar Sin, bayan da ya saurari rahotanni daga tawagogin aikin daidaita sassan tattalin arziki guda 2.

Ya ce daidaituwar tattalin arziki ya danganta da yanayin hada-hadar kasuwanni, don haka ya buƙaci a kara azama, wajen rage wahalhalun da sashen hada-hadar kasuwannin ke fuskanta, yayin da ake ƙara faɗaɗa harkokin zuba jari, har a kai ga samar da damammakin bunƙasa kasuwanni, da ƙarfafa ƙwarin gwiwarsu.

Li Keqiang ya ce ya dace a kara azama wajen kammala manyan ayyuka, da faɗaɗa hada-hadar kuɗaɗe bisa tsare-tsare da aka tanada gwargwadon buƙatun gida.

Ya ce gwamnati za ta tallafawa buƙatun al’umma na samun muhalli, da kyautata muhallin al’umma, da yin kyakkyawan amfani da manufofi, ta hanyar aiwatar da manufofi mafiya dacewa da birane daban-daban.

Mai Fassarawa: Saminu Alhassan