Firaministan Sin ya jaddada muhimmancin ɗorewar bunƙasar tattalin arzikin ƙasa

Daga CMG HAUSA

Firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya jaddada muhimmancin ɗaukar ƙwararan matakai domin haye wahalhalu don tabbatar da samun bunƙasuwar tattalin arzikin ƙasa mai ɗorewa, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci taron tattaunawar majalisar gudanarwa ta ƙasa a ranar Litinin.

Taron ya gabatar da muhimman ɓangarorin da za a mayar da hankali a cikin rahoton ayyukan gwamnati na wannan shekara ga hukumomin da abin ya shafa na majalisar gudanarwar ƙasa da ta kananan hukumomi, kana ya buƙaci a aiwatar da kudurorin yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa, tattalin arziki yana fuskantar sabbin matsin lamba da ƙaruwar ƙalubaloli, taron ya jaddada buƙatar haɗa ayyukan kandagarkin annobar COVID-19 da na bunƙasa cigaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al’umma tare, kana ya jaddada buƙatar bayar da fifiko wajen tabbatar da ɗorewar bunkasuwar tattalin arziki zuwa matsayin koli.

Daga ƙarshe, ƙasar Sin za ta ci gaba da sa lura game da sauye-sauyen da ake samu a yanayin tattalin arzikin duniya, da yin sauye-sauye a manya da kananan manufofin tattalin arziki, da yanayin gudanar ayyukan kasuwannin muhimman kayayyakin buƙatu, da kuma tasirin da zasu haifarwa ƙasar Sin.

Taron yace, za a tabbatar da dorewar samar da makamashin kwal da lantarki. Sannan za a tabbatar da cikakken aiwatar da manufofin da zasu taimaka wajen magance wahalhalun da kamfanoni zuba jarin waje da kuma kamfanonin kasuwancin ƙetare ke fuskanta.

Fassarawa: Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *