Gidauniyar Isah Wali ta jagoranci ƙungiyoyi wajen koya wa masu tallace-tallace sana’o’i

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Gidauniyar Isah Wali Empowerment Initiative IWEI ta gajoranci gamayyar ƙungiyoyi bakwai na tallafa wa al’umma musamam matasa mata da maza koyawa ‘yan talla 50 a bakin titi mata da maza, sana’oi’n dogaro da kai domin rabasu da talla da barace-barace akan titi kamar dai yadda jami’ar ayyuka na musamman a gidauniyar IWEI Madam Bridget Idoko ta bayana a lokacin horas da ‘yan talla 50 sana’o’in dogaro da kai da aka gabatar a makon da ya gabata a ɗakin karatu na Murtala Muhammad dake Kano.

Daga cikin gamayyar qungiyoyin da suka horas da waɗannan matasa akwai Ummahani Salam Foundation da Zainudeen Abdulsalam wanda ke a matsayin babban jami’i a cikinta, wanda ya ce da kafuwarta zuwa yau sun horas da matasa sama da 200 musammam marayu da ‘yan talla akan titi da yara marasa galihu.

Kamar yadda shi ma shugaban jami’i a Ƙungiyar Mu Farka Youth Development ya bayyana irin yadda ƙungiyarsa take aiki na taimakawa yara ‘yan talla don horas da su sana’oin dogaro da kai.

A ƙarshe shugabar kula da ayyuka ta gidauniyar Isah Wali, IWEI ta ce daga cikin sana’o’in da aka koyawa waɗannan ‘yan mata akwai ɗinkin jaka, haɗa sabulai da turaruka da kuma haɗa audigar mata da dai sauran sana’o’i da aka koya musu.

Ta yaba wa ƙungiyar Farawa da Kasamu Girls, sai Mona Hand and Hand, Salosalilu kan haɗin kan da suka bayar na IWEI ta jagorance su wajen horar da ‘yan talla da almajirai 50 sana’o’in dogaro da kai da neman gwamnati ta taimaka wajen irin wannan aiki ko wane mataki na mulkin Nijeriya.