Gwamnati za ta soke wasu manhajojin ba da rance saboda cuzguna wa ‘yan Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce za ta soke manhajojin ba da rance gida biyu saboda suna cuzguna wa ‘yan Nijeriya.

Gwanatin ta bayyana cewa, su dai waɗannan manhajoji da za ta dakatar da su manhajoji ne halastattu da aka yi wa rajista kuma sannan ta saki wani jerin sunayen haramtattun manhajojin ba da rance da suke aiki a ƙasar nan.

Hukumar kare masu amfani da kaya/mai saye (FCCPC) ta bayyana haka a ranar alhamis ɗin da ta gabata.

Inda suka ƙara da bayyana sunayen manhajojin rancen na yanar gizo waɗanda suka ƙi yin rajista a ƙarƙashin dokokinsu da kulawarsu.

A cewar Babban jami’in Zartaswa na hukumar FCCPC, Babatunde Irukera.

Mista Irukera ya ƙara da cewa, a halin yanzu dai sunayen waɗancan gurɓatattun manhajojin ba da rancen suna nan a rubuce a shafin yanar gizo na hukumar FCCPC.

Kuma a cewar sa, sai kamfanonin da suka yi biyayya da tsarinsu da dokokinsu kaɗai aka bari su cigaba da gudanar da harkokinsu a Nijeriya.

Irukera ya ba wa ‘yan Nijeriya shawara a kan su dinga yin taka-tsan-tsan da wajen zaɓar hanyar ba da rance ta intanet musamman manhajojin da suke cikin jerin sunayen ingantattun manhajojin ba da rancen da hukumar ta wallafa.

Wasu daga cikin kamfanonin ba da rancen da aka soke su na har abada sun haɗa da Sycamore Integrated Solutions Limited and Orange Loan, da Purple Credit Limited, tare da manhajojinsu wato — ‘Getloan’ da ‘Camelloan.’

Daga ƙarshe, Irukera ya bayyana cewa, a halin yanzu hukumarsu tana kan bincike da bibiyar waɗannan haramtattun manhajojin domin a cewar sa, kamfaninin suna amfani da manhajojin rancen don jan hankalin masu neman rance kuma su aikata musu haramtattun abubuwa a gare su.

Majiyarmu ta rawaito cewa a halin yanzu dai ƙasar Nijeriya ta ba da rahoton tana da kimanin manhajojin rance guda 180 waɗanda halastattu ne kuma hukumar FCCPC ta san da zamansu, kuma ta ba su damar yin harkokinsu a Nijeriya.

A halin yanzu kuma gwamnatin ta ba da wa’adi ga kamfanonin ba da rancen da ba su yi wa manhajojinsu rajista ba da su yi ko su fuskanci abinda zai biyo baya.