Kotu ta yanke hukuncin kisa a kan ɗan sandan da ya kashe Bolanle Raheem a Legas

Babbar Kotun Jihar Legas ta yanke wa ɗan sanda, ASP Drambi Vandi, hukuncin kisa bayan da ta same shi da laifin kashe lauyar nan, Mrs Omobolanle Raheem a Legas.

A ranar Litinin Kotun mai zamanta a yankin Igbosere a Legas, ta ce dakataccen jami’in zai baƙunci lahira ne ta hanyar rataya.

Aƙalin kotun, Ibironke Harrison, ya ce mai gabatar da ƙara, wato Gwamnatin Jihar Legas, ta gabatar wa kotun ƙwararan hujjojin da suka tabbatar da aikata laifin da ake zargin jami’in da shi.

“Kotu ta sami wanda ke kare kansa da laifi guda ɗaya, wato kisa. Za a rataye ka a wuya har sai ka mutu,” in ji alƙalin a lokokacin da yake karanto hukuncin.

Idan dai za a iya tunawa, a baya Gwamnatin Jihar Legas ta gurfanar da Vandi a kotu kan zargin harbe wata lauya mai ɗauke da juna-biyu da bindiga a ƙarƙashin gadar Ajah a ranar 25 ga Disamban 2022 wanda hakan ya yi ajalinta.

Kotun ta ce laifin da mai kare kansa ya aikata ya saɓa wa Sashe na 223 Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Legas na 2015.