Man fetur (1800-1950)

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Masu hikima wajen sarrafa harshe da masu falsafar rayuwa sun fassara, kuma sun yi tambihin ma’anar kalmar tarihi daga dukkan abubuwan da suka faru a wannan doro na duniya na zahiri ga shi kan sa bil’adama tare da yanayin da yake ciki, aka kuma tattara shi aka adana, gudun kada ya salwanta, domin amfanin al’umami masu zuwa nan gaba.

Tambayar a nan, mene ne man fetur? ’Yan kimiyya suka bayyana a matsayin man fetur ya zama gama gari kamar jamfa a Jos, waɗanne dalilai ne suka kai shi wannan matsayi? Domin sauƙaƙa bayani man fetur, makamashi ne da zai bayar da wata daga ɗanyen man fetur da ake kira ‘Crude Oil’ (wato ɗanyen mai), wanda ya samo asali daga siyasar makamashin kwal (Coal) da ‘Kerosene’, wato kalanzir, waɗanda jama’a suka runguma a matsayin abubuwan rayuwa.

A ƙarni na 19, wato shekara ta 1800 zuwa shekara ta 1900, kimiyar samar da kalanzir daga ɗanyen man fetur ta kankama, saboda haka fafutukar neman ɗanyen man fetur ta bazu a duniya. A wancan lokaci ta fara tashe, kuma hankalin duniya ya koma kansu, suka zama su ne masu faɗa a ji, ba don komai ba sai irin kuɗaɗen shiga da suke samu daga ƙasashen waje.

Kuɗaɗen shiga daga ɗanyen Man fetur ya samar da attajirai a waɗannan ƙasashe da kuma dillalai a sauran ƙasashen duniya kaɗan daga cikinsu su ne Charles Koch, David Coch, Phillip Anshcutz, George Kaiser, William Hawkins Abbott, Boots Adams, John Dustin da dai sauransu. Hakan kuma ya sauya tsarin masana’antu masu ƙera ababan hawa, motoci da babura suka kunno a duniya. Mutanen duniya suka shiga gasar da kuma tsere wajen mallakar ababan hawa.

A tarihin duniya babu wata kadara da ta yi tasiri a rayuwar bil’adam daga wannan lokaci -1800 zuwa 1900, kai har zuwa yau. Rayuwa kacokan ta dogara ga wannan kadara, wato man fetur da gas da kuma dangoginsu. Kasuwar ɗanyen man fetur da gas su suke juya harkoki da al’amuran duniya, walau ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewar al’umma.

Dukkan yaƙe-yaƙe da suke gudana tun kafin yaƙin duniya na ɗaya da na biyu da sauran futuntunu a loko da saƙo na duniya suna da alaƙa da wannan kadara a fili ko a voye. Masana’antun ƙere-ƙere na makamai da cinikinsu na da alaqa da waye zai mallaki wannan kadara ta fuskar bincikowa ko haqowa ko tace shi, daga nan a shiga dakwansa da dillancinsa a sassa na duniya har ya kai ga rarraba shi zuwa ɗaiɗaikun jama’a jama’ar da ta kai sama da Biliyan takwas.

Hatta siyasar aƙida ta dimukraɗiyya da markasanci da kwamanisanci da kuma ’yan baruwanmu da gabasanci ko yammananci sai Musulunci ko Kiristanci ko ma babu addini sun kafu da kuma yaɗuwarsu daga hasashen da kuma hangen samun wannan kadara ta man fetur da gas. Wannan ta sa ƙasashen Yammacin Turai, kamar Turawan Ingila da na Faransa da na Portugal da Jamus da Holland da na Italiya da dai sauransu suka mamaye Afirka.

Sai da suka gama bincikensu tsaf, suka tabbata da ina-da-ina ake da wannan kadara ta man fetur da gas sannan suka fara tunanin ba wa ƙasashen ’yancin kai tun da sun samar da yaransu ta yadda ko da sun tafi, yaran za su gudanar da ayyukan da suke so.

Idan kuka biyo mu sannu a hankali cikin wannan fili na Makamashi, za ku karanta rawar da ɗanyen man fetur da duk dangoginsa, kamar shi kansa tataccen man fetur da gas da kalanzir da man jiragen sama da na ruwa da sauran sinadarai da ake yin magunguna na mutane da na dabbobi da takin zamani da mayuka na mata da sauran mutane ’yan ƙwalisa, suke takawa.

Kamar yadda na ce, za ku karanta ƙulle-ƙullen da aka yi a Sudan da Masar da Libia da Najeriya da Ghana da Angola da Kenya da Kongo da Maruritaniya kai har zuwa Afirka ta Kudu. Za mu ji irin rawar da man fetur yake takawa a waɗannan ƙasashe.

Za mu ga yadda mai doki ya koma kuturi; fatara da talauci da jahilci da yaƙe-yaƙe da faɗace-faɗace na addini da ƙabilanci da tashe-tashe hankali na a raba da juye-juyen mulki na sojoji da na ’yan siyasa da ’yan daba da ’yan bindiga daɗi da cin hanci da rashawa da ci da ceto da kuma wawason dukiyar gwamnati ta hannun waɗanda aka ba wa amana.

Hada-hadar man fetur a Nahiyar Afirka makaranta ce babba da za mu shiga cikinta, idan Allah ya kai mu gaba lafiya, za mu feɗe biri har bindinsa. Saboda haka mu ke gayyatarku da ku biyo bashi. Saura da me? Na ke cewa a yi harkokin rayuwa cikin ƙoshin lafiya, amin summa amin.