Jarumi Abba El-Mustapha ya zama Shugaban Hukumar Tace Finafinai

Daga AISHA ASAS

Tun bayan sauya gwamnatin Jihar Kano, ake muhawara kan wanda za a ba wa ragamar shugabantar Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, lamarin da ya zama abin tattaunawa a shafukan sada zumunta.

Duk da mutane da dama sun faɗi ra’ayinsu kan waɗanda suke hasashen za su iya ɗarewa kujerar shugabancin hukumar, kamar Sunusi Oscar 442, Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, Salisu Muhammad Officer, sai dai da yawa sun aminta da cewa, a dukka mutanen da ake zayyanowa ba wanda ake hasashen zai iya danne fitaccen jarumi Abba El-Mustapha sakamakon irin rawar da ya taka a siyasar Kwankwasiyya da kuma kusancin da yake da shi da sabon gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kwatsam sai labari ya bayyana cewa, gwamnan jihar ya naxa jarumin Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano kamar yadda xinbin al’umma suka yi hasashe.

Ɗimbin jama’a daga ciki da wajen masana’antar finafinai Kannywood sun taya murna ga jarumin tare da yi masa fatan jagorantar hukumar cikin nasara da kuma kauce wa matsalolin da tsohon shugaban hukumar ya haifar wa masana’antar da jarumanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *