Cibiyar Kannywood Foundation ta taya jarumi El-Mustapha murna

Daga WAKILINMU

Cibiyar Kannywood Foundation ta yi taya murna ga jarumi Abba El-Mustapha naɗin da Gwamnan Kano ya yi masa kwanan nan.

Gwamna Abba Kabira ya naɗa Abba El-Mustapha ne a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, wato KSCB.

Cikin sanarwar da ta fitar mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na cibiyar, M.K Maikaba, cibiyar ta ce “Gaba ɗayanmu shugabani da ‘ya’yan wannan cibiya na matuƙar farin cikin samun tabbacin wannan muhimmin labari.

“Don haka muke yi wa Allah Mai Girma godiya, sannan muna son mu nuna wa Mai girma zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Eng. Abba Kabir Yusuf dangane da irin wannan karamci da ƙauna da ya nuna wa wannan masana’anta.

“Muna taya shi addu’a Allah ya taya shi bisa duk wata niyya ta alheri da ya bijiro da ita Dan ciyar da jihar gaba.

“Haƙiƙa ɗora Abba na Abba a kan wannan kujera ya kasance an ɗauki ƙwarya an ɗora akan gurbinta. Jajircewa da kwarjini wannan da namu ya tabbatar mana da wani haske da ya nuna mana hanyar cigaba ɗoɗar a wannan masana’anta,”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *