Maraba da shekara ta Hijira 1444

Bayan godiya da yabo ga Allah. Ina amfani da wannan dama mu faɗakar wa junanmu cewa zuwan shekara ta Hijira 1444 wata alama ce mai nuna a kullum muna bankwana da wannan duniya kuma muna fuskantar tafiya ga rayuwa ta har abada wacce ake guzurinta tun a nan duniya.

Tabbas al’ummar Musulmai mu na da manyan ƙalubalai a rayuwa wanda ba kowa ke gane hakan ba sai wanda Allah ya haska ma wa.

Haɗin kai da taimakekeniya a yau sun wuyata. Inda rarrabuwa da kuma rashin daraja juna ta yawaita. Da fatan inda duk Musulmai muke da yawan bayyana matsalolin cikin mu bayan mun sani cewa umurni ne Allah ya bayar cewa kar mu rarraba.

Allah ka haɗa kawunan dukkanin mu tare da ƙauna da kare martabar junanmu.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519/08080140820.