Masu ruwa da tsaki sun koka kan garƙame iyakar Nijar

Daga Jamil Gulma a Kebbi 

Tun lokacin da Shugaban Ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tunubu, wanda kuma shine Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ya ayyana cewa, akwai yiwuwar ƙaddamar da yaƙi da sojojin da suka hamɓarar da zavavven Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Bazoum, idan sulhu ya gagara, ba shakka wannan ya tayar da  hankalin dubban ’yan Nijeriya mazauna ƙasar ta Nijar da kuma al’ummomin da ke zaune kan iyakokin ƙasashen biyu kuma ya sanya su shiga wani yanayi na tashin hankali.

Wakilin Bleuprint Manhaja ya zagaya  waɗansu garuruwa da ke maƙotaka da Nijar din kuma ya zanta da mazauna waɗannan yankunan, inda Alhaji Abubakar Lauwali wani mai safarar abinci a hanyar Bachaka ya bayyana cewa a kan  wannan iyakar ba yadda za a hana hulɗa tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar saboda uwa ɗaya uba ɗaya suke, akwai daɗaɗɗiyar dangantaka ta auratayya da cinikayya da sauransu, tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka don haka ko da an rufe iyakokin ba zai hana su hulɗa ba sai dai rufewar ta gurgunta harkokin da dama.

Malam Sha’aibu Mungadi, ɗan jarida kuma mai fashin baƙi, ya bayyana cewa, a harkar diflomasiyya ba a amfani da ƙarfin soja a matakin ƙarshe, abinda ya fi kyau shi ne hawa teburin sulhu, saboda ko yaƙin aka yi sai an sake dawowa kan teburin sulhu.

“Maganar gaskiya ita ce, Shugaba Tunubu Bayerabe ne kuma ba shi ba babu wani Bayerabe da ya san dangantakar Sokoto da Ƙasar Nijar, akwai auratayya tsakanin jihohin Sokoto da Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Yobe da Borno da Ƙasar Nijar ba an yi auratayya an assasa zuri’a, wacece shi Tunubu bai san da wannan ba yana can Kudu zamansa, saboda haka yin haka ba a kyauta wa Arewa ba kuma bai kyautawa Nijeriya ba,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa maganar yanke wutar lantarki ga Nijar sava alƙawari ne, sava yarjejeniya ce da aka yi tun shekaru masu yawa bisa ga sharadin Nijar ta bari a yi dam ɗin Ka’inji, saboda kowace ƙasa ta sami wuta wanda idan Nijar ta yi wannan dam xin akan Kogin Neja (river niger) Nijeriya ba za ta samu wadataccen ruwan da zai isa ba, saboda haka aka tsaya a kan haka.

Wannan ƙudirin dai na Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ƙarƙashin jagoranacin Shugaban Tunubu yana kan shan suka daga kowane ɓangare a Nijeriya tun kama daga haɗaɗɗiyar ƙungiyar malaman addini, ƙungiyoyin sa kai, ɗaiɗaikun masana farar hula da sojojin da suka ajiye aiki, uwa-uba har zauren majalisar wakilai da dattawan tarayyar Nijeriya.

Ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar gundumar mazavar Kebbi ta Tsakiya, Sanata Adamu Muhammadu Aliero, ya bayyana cewa, tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka akwai alaka ko dangantaka mai ƙarfi tsakanin Nijeriya da Nijar musamman daga arewacin Nijeriya tun kama daga ta auratayya, kasuwanci da sauransu.

Ya bayyana cewa rufe kan iyaka ba ƙaramin kassara ’yan kasuwa ya yi ba, saboda yanzu haka akwai ɗaruruwan  motoci a kan iyakokin ƙasashen biyu  ɗauke da dukiyoyi da suka halaka sanadiyyar rufe iyakokin wanda ba ƙaramin koma-baya ba ne ga arewacin ƙasar ba. Saboda haka an ko kuma a na cutar da wani ɓangare ne na Nijeriya.

Ɗaya daga cikin shugabannin ’yan kasuwa a Ƙaramar Hukumar Mulki ta Arewa, Alhaji Sani Mai Gadaje Kangiwa, wanda kuma kasuwancisa ya ya ta’allaƙa ne da cinikayya tsakanin ƙasashen biyu, ya bayyana cewa yanzu haka mutanen da rufe iyakokin ya gurgunta suna da yawa, saboda haka ya bayyana cewa rufe iyakokin ba shi ne mafita ba sai idan akwai wata manufa.

Yanzu haka sanadiyyar rufe iyakokin ya ƙara kawo tarnaƙi ga magidanta sanadiyyar durƙushewar kasuwancisu, bayan rufe iyakokin ga kuma matsin tattalin arziki inda abinda za a ci a waɗansu gidaje ya gagara.

Wani ɗan kasuwa da bai so a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa su kam rufe iyakokin bai hana su gudanar da kasuwancinsu ba saboda ba za su zauna yunwa ta tarwatsa gidajensu ba saboda haka sun zaɓi ɗaukar matakin kai-komo ta ɓarauniyar hanya wajen hada-hadarsu.