Kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya yi murabus

Daga BASHIR ISAH

Jose Peseiro ya murabus a matsayin mai horar da ‘yan wasan Super Eagles na Nijeriya.

Peseiro ya sanar da hakan ne a shafinsa na X a ranar Juma’a, 1 ga Maris, 2024.

Ya ce kwatiraginsa da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta ƙare, kuma ba a ƙulla sabo ba.

Ya bayyana watanni 22 da ys shafe a matsayin babban kocin Super Eagles, a matsayin sadaukarwa.

Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen nuna godiya ga ‘yan wasan na Super Eagles da hukumar NFF, yana mai cewa a duk lokacin da aka buƙace za a same shi.