Masu zanga-zanga sun daka wawa kan babbar mota mai ɗauke da taliyar BUA a Zaria

Daga BASHIR

Wasu masu zanga-zanga a yankin Dogarawa a Zaria, jihar Kaduna, sun daka wawa kan wata babbar motar kamfanin BUA mai ɗauke da kayan taliya a kan babbar hanyar Zaria zuwa Kano.

Wannan na zuwa ne kimanin mako guda bayan da wasu jama’a suka daka wawa kan wata babbar mota mai ɗauke da kayan abinci a yankin Sulej, Jihar Neja.

Majiyarmu ta ce motar BUA ɗin ta baro Kaduna ne da nufin zuwa Abuja inda ‘yan daban suka tare hanya suka far mata.

Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 3.15 na rana a daidai lokacin da direban motar ya tsaya don yin salla.

Ya ce tsayawar direban ke da wuya sai masu zanga-zangar suka shiga ɗibar katan-katan na taliyar da motar ke ɗauke da ita.

Haka nan, ya ce lamarin abin takaici ne saboda a cewarsa, irin haka bai taɓa faruwa ba a yankin.

“Ko kwali guda na taliyar ba su bari ba, duk sun kwashe,” in jibshi.

Bayanai sun ce daga bisani an tura ‘yan sanda yankin inda suka samu kama wasu daga cikin waɗanda suka aikata wawar.