Samun haɗin kan marubuta ne babban burina – Rufaida Umar

“Addu’a ce sirrin samun nasarata a gasar rubutu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kamar yadda rayuwa take nuna kowa da rabonsa a duniya, kuma kowa da irin tanadin da ubangiji ya yi masa. Haka yake kasancewa a rayuwar marubuta, kowa da yadda harkokin rubutunsa ke tafiya. Wani cikin sauri da samun nasara akai akai, wani kuma sai ya yi aiki tuƙuru kafin ya cimma nasarar da yake nema. Rufaida Umar Ibrahim na ɗaya daga cikin irin waxannan marubuta da za a iya kira da ƴan baiwa, saboda yadda suke samun nasarori cikin rubuce-rubucensu, musamman ma dai a gasar rubutun Gajeren Labari da ake shiryawa lokaci lokaci. Tana daga cikin gwarazan gasar Hikayata ta BBC Hausa a 2020. Ita ce ta farko a gasar Jaridar Aminiya a 2021. Kuma ita ce ta biyu a gasar Ɗangiwa ta shekarar 2022, wacce ba a jima da ba da sakamako ba. A zantawarta da wakilin Manhaja Blueprint, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta shaida masa sirrinta na samun nasara da kuma burinta a harkar rubutun adabi.

MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kan ki.

RUFAIDA: Sunana Rufaida Umar Ibrahim. Ni marubuciya ce, kuma ƴar kasuwa. Ina sayar da kayan sawa na yara maza da mata, da kuma suturu na mata. Ni matar aure ce, kuma ina da yara uku.

Ko za mu san wani abu game da tarihin rayuwarki?

An haife ni a Jihar Kano a Ƙaramar Hukumar Dala, a ranar 16 ga watan Junairu 1995. Na kammala karatuna na firamare a shekarar 2005 a makarantar firamare da ɓangaren rainon yara da ke Yandutse. Na kuma samu nasarar kammala karatun sakandire a shekarar 2011, a Kwalejin Yandutse. Daga bisani na shiga Kwalejin Ilimi ta Tarayya, wato FCE Kano, inda na samu shaidar karatu ta NCE a vangaren ilimin koyar da sanin halittu da ilimin addinin Musulunci, na kammala a shekarar 2022.

Me ya ja hankalinki ki ka fara tunanin zama marubuciya?

Yawan karance-karancen littattafan Hausa ne ni ma ya ja ra’ayina ga fara rubutu.

Wanene ya fara taimaka miki lokacin da za ki fara rubutu?

To, gaskiya kasancewar na fara rubutu ne tun kafin na fara yi a soshiyal midiya, ina zama ne na rubuta a littafi na ba ƴan gidanmu su karanta. A lokacin da na soma a soshiyal midiya, na samu masu ƙarfafa min gwiwa da dama a marubuta da cin gyarana a inda na yi kuskure. A zauren Duniyar Marubuta dake fesbuk, akwai Adamu Maikudi, yana cikin mutanen farko da suka zama tamkar malamaina a duniyar rubutu, akwai Safiyya Ummu Abdul, sai Jibrin Adamu Rano da sauransu, waɗannan na daga cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen ganin rubutuna ya inganta sosai.

Wanne labarin ki ka fara rubutawa, kuma wanne ƙalubale ki ka fuskanta lokacin rubutawa?

Littafin ‘Mahaifiya’ shi ne littafina na farko da aka fara sanina da shi. Sai kuma labarin ‘Ba Zan Barki Ba’ wanda shi ƙaramin littafi ne. Sannan zan iya cewa, na fuskanci ƙalubalen rashin sanin ƙa’idojin rubutu, da ma rashin bincike kafin a yi magana game da wani abu a rubuce.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai nawa?

A gaskiya na rubuta littattafai fiye da 10, a ciki akwai ”Yar Bariki’, ‘Mijin Mace Ɗaya’, ”Ɗan Adam’, ‘Daraja Ɗaya’, ‘Muƙaddari’, ‘Rumfar Kara, ‘Dukan Ruwa’, ‘Rayuwar Hamida’, ‘Ruɗin Shaiɗan’, ‘Fitar Tsiro’, ‘Amadu’, ‘Bazan Barki Ba’, da sauran su da dama.

Littafina na ‘Ƙarfen Ƙafa’, labari ne akan rayuwar wata matashiya mai suna Ramlat, wacce ta haɗu da nadama da da-na-sani a rayuwarta bayan bijirewar zaɓinta na farko a aure, Hilal. A ƙarshe ta auri mutumin da ta ƙwallafa rai a kansa, Aliyu, ba tare da son ran iyayenta da duka ýan’uwanta ba. Sanadiyyar wannan aure ta haɗu da qalubale iri-iri, ciki har da duka da rashin sanin darajarta.

Shi kuma littafin ‘Dukan Ruwa’, labarin Hajiya Maryama ne. Mace ce mai son kanta da ƙyashi da hassada wanda ta lulluve shi da zallaryaudara da makirci, ta zama mai fuska biyu har ta kai tauraruwarta kaɗai ke haskawa a idanun mijinta Alhaji Yusuf, wanda tun bayan rasuwar abokiyar zamanta Fatima, bai ƙara kallon wata ɗiya mace da sunan so ba. ‘Yan riƙonta su biyu ne idan ka ɗauke yaran da ta haifa da cikinta, wato Humaira ɗiyar marigayiya Fatima da kuma Ummita ƴa ga qanin Alhaji Yusuf.

Sulaiman wanda shi da matarsa da jaririn da aka haifa masa suka rasu sanadin gobara. Soyayyar da take nuna musu a zahiri da kuma kulawa irin wanda ko yaranta ba ta nunawa hakan, ya ƙara ɗaukaka darajarta a idanun mijinta da ýan uwansa. Babu wani da ya tava hasaso akwai ɓoyayyen sirri da manufa a zuciyar Hajiya Maryam game da yaran. Asirinta bai tashi tonuwa ba sai da ta sanya aka yi garkuwa da su domin son cikar burinta na ganin ta mallake dukiyar Alhaji Yusuf ya zamana daga ita sai yaranta ne za su mora.

Hakan ya yi sanadin da har aka keta haddin Ummita ta samu ciki. Ya kuma yi sanadin fasa aurenta. Ta hanyar asiri Hajiya Maryama ta jefawa Humaira tsanar kowanne ɗa namiji a zuciyarta. Duk a dalilin rufewar da idanun Hajiya Maryama ya yi na son cikar burinta, ta zama sanadiyyar mutuwar iyayen Ummita da kuma ‘Mahaifiyar Humaira.

A qarshe, reshe ya juye da mujiya. Ta ruguza rayuwar ƴaƴanta da kanta, asirinta ya tonu a wurin mijinta da danginsa. Ta dawo babu dukiyar babu kuma mulkin, komai ya ƙare ta faɗa cikin tsananin rayuwa da ya jefa ta cikin tafkin nadama da dana sani. Yaran da ta kashe kanta don ta inganta rayuwarsu, suka tsane ta, ta kuma rasa gatan miji.

Shin kin taɓa buga wani daga cikin littattafanki ko duk a online ki ke sakewa?

Ban taɓa buga labarina ba. Sai dai ko gajerun labaraina da na ci gasa da su waɗanda kuma ake haɗe su waje guda a buga da na sauran marubuta.

Wacce riba za ki ce kin samu daga rubutun da ki ke yi, ana samun ciniki daga masu karatu na online?

Alhamdulillah, riba ta farko da na samu a rubutu shi ne isar da saƙo. Daidai gwargwado saƙonnin da nake rubutawa ta cikin labaraina yana isa ga al’umma. Sai kuma riba ta ɗaukaka, inda ban je ba, labarina ya je kuma ya faɗakar. Sai riba ta ciniki, ina samu daidai gwargwado daga litattafan da nake sayarwa a onlayin.

Wanne ƙalubale marubutan onlayin suke fuskanta, wajen sayar da rubutun su da matsalar satar fasaha?

Babban ƙalubalen da muke fuskanta wurin sayar da litattafanmu a yanar gizo bai wuce masu buɗe zaure ko group suna tattara litattafanmu na kuɗi su na sayar da su akan farashin 200 ko ƙasa da hakan ba. Wannan abu ne da ke ci mana tuwo a kwarya, ko kuma ka ga mutum ya saya ya fitar. Sai kuwa masu satar fasaha, a yanki wani ɓangare na labarinka a rubuce. Sai dai gaskiya ni ban taɓa haɗuwa da irin wannan matsalar ta satar fasaha ba.

Shin kina ganin fitowar manhajojin sayar da littattafai na online suna da tasirin da za su kawo lalacewar kasuwar littattafai?
Abin da mutane za su kula da shi, shi ne, yanzu kaso mafi yawa daga cikin waɗanda suke karanta bugaggen littafi, sun koma karatu a waya. Wasu ta hanyar sauraro wato audio, wasu kuwa ta hanyar karantawa a matsayin shafi shafi ko kuma a dunƙulallen Document.

Tun da yanzu zamani ne ya zo da karatu ya koma onlayin. Ina ganin ya kamata a haɗe ƙarfi da ƙarfe wajen fiddo da wasu tsaruka masu kyau da kowa zai ci gajiyarsa.

Kina daga cikin marubutan da suka samu nasarori a gasar rubutun Gajeren Labari da ake shiryawa, ko za mu san irin nasarorin da ki ka samu?

Alhamdulillah. Na soma shiga gasar gajerun labarai tun a shekarar 2018, inda muka haɗu muka yi labari tare da Ummu Abdul muka aika BBC Hikayata, ba mu yi nasarar fitowa cikin zakaru ba, sai dai labarin ya samu fitowa cikin waɗanda suka samu jinjina har aka karanta. Sai a shekarar 2020 na shiga gasar Hikayata da labarina na FARAR qAFA inda na zo ta uku.

A wannan shekarar dai na shiga gasar Aminiyatrust da labarina na DIMOKURAxIYYAR TALAKA, na zo ta ɗaya. A shekarar 2021 na shiga gasar Tsuburin Gobir da labarina mai suna GYARA KAYANKA nan ma na yi nasarar zuwa ta Uku. Sai Gasar ɗangiwa da na shiga a shekarar 2022 wanda aka yi bikin karramawar a 2023, inda na samu zama ta biyu da labarina mai suna SON ZUCIYA.

Menene sirrin samun waɗannan nasarori da ki ka samu?

Duk gasar da zan shiga, ina sanyawa a raina ne, nasara daga Allah take. Bayan iyaka ƙoƙarin da nake yi wajen ganin na tsaftace rubutuna, ina kuma bayarwa a taya ni ƙyaran ƙa’idojinrubutu da kuma shawarwari, sai kuma addu’a. Dukkan nasara tana tare da addu’a. Wannan shi ne abin da nake ƙudirtawa a raina.

Wacce shawara za ki bai wa sauran ýan’uwa marubuta da ke sha’awar shiga gasar marubuta?

Shawarar da zan ba su, kar su yi gaggawa, kar kuma su yi abu ba tare da sanin iliminsa ba. Alhamdulillah, na ga ɗan uwa kuma malamina Jibrin Adamu Rano, yana iyaka ƙoƙari wajen ganin ýan’uwana marubuta sun ci wannan moriyar ta sanin makaman rubuta gajerun labarai ta hanyar ba su shawarwarin da suka kamata. Kar mutum ya yi girman kai, ko ɗan shekaru goma ne ya fi ka a sanin ilimi, ka maida hankali wurin koyo. Kowannenmu koyo yake, ba iyawa ce ko dabararmu ba. Allah ya sa mu dace.

Na ji daɗi fiye da zato, na sani ba yin kaina ba ne, har da addu’a. Alhamdulillah, ban fi kowa ba. Ina yi wa kowa fatan samun fiye da wanda na samu.

Kasancewarki malama, ýar kasuwa, kuma uwa, yaya ki ke tsara lokacinki har ki samu damar yin rubutu?

To, ni rubutu ina yin sa ne duk lokacin da na samu ƴar dama, zan iya yi cikin dare, ko da asuba ko kuma idan na kammala ayyukana. Gaskiya tsara lokutan gudanar da kowanne ba ya bani wahala.

Wasu marubuta na kokawa da rashin samun sharhi ko tsokaci daga masu karatu, yaya ki ke ji idan kin fitar da rubutu amma ba ki samu sharhin da ki ke sa ran samu ba?

Ni dai bana fuskantar rashin masu sharhi a labaraina, Alhamdulillah, ba na damuwa da ko mutum biyar ne kacal masu bibiya su yi sharhi, a hankali su ke qaruwa su ninka fiye da tsammanina.

Yaya alaqarki take da masu bibiyar littattafanki?

Muna zumunci kuma muna mutunta juna.

Wanne hasashe ki ke da shi nan gaba a harkar rubutun adabi?

Babban burina a duniyar adabi bai wuce a samu haɗin kai tsakanin marubuta ba. A kuma gina wani tsari wanda za a yi amfani da shi wajen magance matsalar masu rubutun batsa.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Komai nisan jifa, ƙasa zai dawo.

Masha Allah. Na gode.

Ni ce da godiya.