Uwar da ta san daɗin sana’a ce ke koyar da ‘ya’yanta – Farida Musa Kallah

“Yana da matuƙar muhimmanci iyaye su cusa wa ‘ya’yansu son sana’a”

(Ci gaba daga makon jiya )

Daga AISHA ASAS

Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Gimbiya na jaridar al’umma, Manhaja. Idan ba ku manta ba, mun yi alƙawarin kawo maku ci gaban tattaunawar da muke yi da fitacciyar ‘yar kasuwa, kuma ‘yar boko, Farida Musa Kallah. Tun daga farko mun fara ne da tarihin rayuwarta, kafin mu gangara kan matakan da ta hau har ya kaita ga nasara a harkar kasuwanci. Hajiya Farida Musa Kallah ta yi muhimman batutuwa kan sha’anin neman na kai, wato sana’a ta kuma bayyana wa masu karatu wasu daga cikin ƙalubalen da ta ci karo da su, da yadda ta yi nasarar kwankwaɗe su. A wannan makon, kamar yadda muka ɗau alwashi, za mu fara da tambayar da muka yi wa Hajiya, wadda wuri bai bamu damar jin amsar daga wurin ta ba. Idan kun shirya, a sha karatu lafiya:

MANHAJA: Ba mu labarin irin nasarorin da ki ka samu a ɓangaren kasuwanci kawo wa yanzu.

FARIDA KALLAH: Alhamdu lillahi. Nasarorin da na samu ba za su ƙirgu ba, duba da cewa, na fara sana’a a falon gidana, ba ma ni da wani ɗaki takamaimai da zan iya ware wa sana’ar, a hakan aka wayi gari na tumbatsa na koma garejin gidana, saboda samun cigaba da wurin ya masu ƙaranci, a haka na sake yin gaba, inda na yi tsalle sai cikin kasuwa, na mallaki shago na farko, na sake ƙarawa da na biyu, na kai ga na uku, har ga shi yanzu Ina shirin mallakar na uku.

Baya ga haka, Ina da katafaren shago a ƙofar gidana, don matan da ba sa iya zuwa kasuwa. An samu rufin asiri daidai gwargwado, an mallaki gidaje da wasu muradun zuciya. Alhamdu lillah!

Ko kin yi nadamar ajiye zancen aiki ki ka rungumi kasuwanci?

Gaskiya ban taɓa nadamar zaɓar sana’a na share zancen aiki ba, saboda sana’a ce ta ba ni ababe da dama, ciki kuwa akwai samun cikakken lokacin kula da iyalina da ni karan kaina, wannan ya sa na gane fa’idar sana’a, domin ni da da nake son aiki, sai naga zan je ne na yi aiki a ƙarƙashin wani, in fita da sassafe, na bar iyalina. Sai na fahimci kamar ban yi tunani ba sosai a lokacin, domin sana’a bata tursasa ni yin wannan ba.

Ina tare da iyalina, komai a gida nake yin sa, musamman ma idan ka yi tsari mai kyau, domin zamani ya kawo sauƙi a harkar kasuwanci, a gida ma sai ka yi ta waya kana kasuwanci da kula da sha’anin sa, ga kuma na’urar CCTV da za ka iya saka wa, daga gida ka dinga kallon duk abinda ke wakana a wurin sana’ar ka.

Don haka gaskiya ban taɓa nadamar rashin yin aiki ba, sai dai ma jin daɗin da nake yi na kai matakin da na ɗdauki ma’aikata da suke aiki a ƙarƙashina, suna samun rufin asiri. Na zama hanyar samar da aikin yi ga mutane, domin a yanzu muna da ma’aikata kusan 40, kuma muna ci gaba da ɗaukar wasu. Gaskiya sai hamdala.

Wacce shawara za ki ba wa macen da ta ce, tana son sana’a, amma ba ta da wani ƙwaƙwaran jari, ko ba ta da jarin kwata-kwata?

To zance na gaskiya jari shi ne sana’a, sai dai bai kamata a ce mace ta rena kaɗan da ta ke da shi a lokacin da zata yi sana’a. Ki duba ki ga abinda ki ke da shi, komai ƙarancin shi, ba za a rasa sana’ar da zai iya yi ba. Sai ki yi nazari ki duba irin wurin da ki ke zama, menene aka fi buƙata ko yawan siya. A ciki sai ki zaɓi wanda kuɗin da ki ke da shi za su iya fara ta.

Bari in bada misali da ruwan leda, wato ‘pure water ‘, Ina yawan bada misali da wannan sana’a, yanzu a yanayin da muke ciki na zafi, mutane na yawan siyan ruwa. Kinga sana’a ce da idan kina da firijin za ki iya yi da ɗan kuɗi kaɗan. Ki sa a kula ko bokiti, ki samu ko almajirarai haka su zauna ma ki a ƙofar gida, su ma ki talla ko su zaga, suna saidawa. Kinga ‘yan na vatarwa za su dinga fitowa, kuma sannu a hankali za a kai ga babba.

Amma sai kiga mace na ƙorafin bata da kuɗi, amma tana da kuɗin sa data ta hau soshiyal midiya, kinga kuwa za a iya cewa tana da kuɗin da za ta iya siyan fiyawata ta fara saidawa. Ba iya sanar ruwa kawai ba, akwai sana’oi da dama da mace za ta iya duba wa ta ga wadda ta dace da kuɗinta, kuma idan ta yi za a siya a unguwar da ta ke zama. Daga nan ne zata fahimci daɗin neman na kai, sai ta dage, ta fara kallon gaba, wanda da ɗan abinda ta tara, sai ta ciyar da sana’ar gaba.

Ta yaya ki ke iya tauna taura biyu a lokaci ɗaya, wato kula da iyali, da kuma kasuwanci?

Da farko dai idan da tsari ba na jin wani zai iya samun tawaya tsakanin waɗannan ababe guda biyu. Abinda ake buƙata, tsara kowanne a ba shi na shi lokaci. A gaskiya ban samu wata matsala ba wurin haɗa kula da iyali da kasuwancin da nake yi, saboda na yi wa kowanne matsaya mai kyau, kowanne daga ciki yana da lokacinsa.

Kasancewar ana cewa, wai mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo, don haka yake da matuƙar muhimmanci ki fahimci tsarin naki gida da kuma sana’ar da ki ke yi, don ganin kin ba wa kowanne muhimmanci da lokacin da yake buƙata, ba tare da kin tauye ɗaya daga ciki ba.

A ɓangare na waɗannan matakai na bi, don haka ban da matsala ta kowanne ɓangare, kuma komai na tafiya yadda nake so.

Wane kira za ki yi ga iyaye kan horar da ‘ya’yansu neman na kansu?

Ai uwar da ta san daɗin sana’a ba ta tava barin ‘yarta hakan kawai. Ai tun da wuri ta ke fara koyar da ‘yarta sana’a don ta san daɗinta da kuma illar rashin ta. Kuma kamar yadda aka ce, uwa ce makarantar farko ga ‘ya’yanta, kinga kuwa sana’ar da ta ke yi kawai ta koyar da ‘ya’yanta zaman banza ba na su ba ne. Duba da cewa mahaifiyarsu ba zaman banza ta ke yi ba, don haka su ma za su ga sana’a a matsayin wajibin su.

Abinda na jima Ina faɗa, ita sana’a daban ta ke, idan an kammala karatu ne, ko ana kan yi, ko ana aiki ne za ka iya yin sana’a kuma idan ka yi za ka ga alfanun ta. Kada ka ce don kana ɗaya daga cikin waɗannan ba za ka iya sana’a ba. Ita sana’a ita ce bata da lokacin gama ta, misali idan aiki ka ke yi, akwai lokacin ritaya, idan kana da sana’a a wannan lokacin ba za ka fara tunanin ina za ka ba, bare kuma su yara, wai a ce don suna karatu ba za su yi sana’a ba, shin kuna da tabbacin za su samu aiki a take bayan kammala karatun? Kuma ma yin sana’ar ta su a lokacin zata iya taimakon ku kanku iyaye, domin a hankali za su kai ga ɗauke ma ku wani nauyi nasu.

Don haka yana da matuƙar muhimmanci iyaye su cusa wa ‘ya’yansu so sana’a tun tasowar su, hakan zai iya zama hanyar da zata ba su rufin asiri.

Wasu na ganin sana’a zata iya hana yaro karatu, don haka sai su hane su da yin kowacce sana’a a ƙoƙarin su na ganin sun mayar da hankali sosai kan karatu. Me za ki ce game da wannan?

To a halin da muke ciki ma zan iya cewa muna bisa gaɓar da bai ma kamata ka hana wa yaronka yin sana’a ba wai don yana karatu. Duba da cewa mutane nawa suna kammala karatun, amam ba aikin yi, suna zaune a gida, saboda ba su da sana’a kuma aikin bai samu ba, sai fa a lokacin ne za su fara tunanin neman sana’a.

Mu kanmu muna ganin irin waɗannan, za ki ga yaro ya gama karatu, an kawo mana CV shi, ana neman mu ɗauke shi aiki, saboda bai samu ba a inda yake tsammanin samu. Kinga kuwa da tun lokacin da suke karatun iyaye sun nuna masu muhimmancin sana’a tare da sa su a hanya, da wataƙila ko da za a kammala karatu ana da wani mudabbari da za ka iya dogaro da shi.

Yanzu ko ɗan harkan nan ta siyar da data, amatsayin ka na ɗalibi za ka iya haɗawa kana yi, da ɗan jari kaɗan, kuma bai tava karatunka. Ga sana’o’i nan da dama da za ka iya yi tare da karatu, ko iya na soshiyal midiya ma kawai za ka samu zaɓi masu yawa.

Kaga ta hakan idan dama ta ƙiya, sai a koma wa hagu. Idan aiki bai samu ba, dama ba ka zama baƙo a sana’a ba. Idan kuwa ya kasance zuciyar yaro ta bushe daga sana’a, bai san komai ba sai karatu, to fa a lokacin da ya kasa samun aiki kowanne irin hali ma zai iya shiga. Da wannan nake ganin ya kamata iyaye su dage ƙwarai wurin tusa wa ‘ya’yansu son sana’a tare da sa su a hanyar yadda za su yi. Idan kuma sun zo da irin wadda suke son yi, idan dai ba illa a ciki, kada a sare masu gwiwa, a ba su ƙwarin gwiwa yadda zai ƙarfafa su, su ƙara dagewa.

Mun gode da lokacin ki.

Ni ma na gode ƙwarai da gaske.