‘Yan bindiga na samun bayanai fiye da yadda muke samu – Dikko Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya ce a halin yanzu ‘yan bindiga na samun bayanan sirri fiye da yadda gwamnati ke samu lamarin dake ƙara dagula ƙoƙarin jami’an tsaro na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a jihar.

“Suna samun bayanai fiye da yadda muke samu”. Inji shi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron gaggawa kan matsalar tsaro wanda ya jagoranta tare da sauran jami’an tsaro dake jihar.

A cewarsa, “Makahon yaƙi ne ake yi da ‘yan bindiga saboda ba ka sanin waye maƙiyinka ko masoyinka saboda wani lokaci duk da masu ba su bayanai muke tare. Saboda haka kowa sai ya zama ɗan sandan kan shi wajen samar da tsaro.

“Muna tattaunawa kan matsalar tsaro amman muna gamawa za su samu dukkan bayanan da aka tattauna,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma ce, har yanzu yana kan bakansa na cewa kowane ɓangare yana da hannu cikin rashin tsaro a Nijeriya.

“Mun kama sarakai da jami’an gwamnati da ke da hannu cikin matsalar tsaro a jihar Katsina, mun kuma samu bayanai da dama dake tabbatar da hakan”. Inji shi.

Har yanzu ‘yan bindiga na ci gaba da addabar wasu ƙananan hukumonin jihar ta hanyar sata da kuma yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

Saboda haka ne masana ke ganin cewa matsalar tana ci gaba da ƙamari duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke cewa suna yi don shawo kan lamarin, sanadiyyar mutanen da ke baiwa ‘yan bindigar bayanan sirrin al’umma.