Zaɓen Ekiti: INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar gwamna

Daga BASHIR ISAH

Hukumaar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fitar da sunayen ‘yan takarar da ake sa ran za su fafata a zaɓen gwamna na jihar Ekiti wanda zai gudana a ranar 18 ga Yunin 2022.

Wannan ya zo ne bayan da INEC ta wallafa bayanan kowane ɗan takara daga ‘yan takarkarun a watan jiya.

INEC ta ce abin da ta yi shi ne ya yi daidaita da abin da Dokar Zaɓe ta tanadar, bayan da aka rufe ƙofar neman fitowa takara ga jam’iyyu siyasa.

Bayanan da INEC ta yi ta bakin babban jami’inta, Festus Okoye, sun nuna an tantace Abiodun Abayomi Oyebanji a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC tare da Afuye Monisade a matsayin mataimakinsa, yayin da aka tantance Olabisi Kolawole a matsayin ɗan takarar PDP tare da Kolapo Olugbenga Kolade a matsayin mataimakinsa.

INEC ta ja hankalin jam’iyyu kan cewa duk jam’iyyar da ta ga babu sunan ɗan takararta a cikin jerin sunayen ‘yan takaran da aka tantance, ta hanzarta ta sanar da hukumar a rubuce, kuma za a yi hakan ne kada ya gaza kwanaki 90 kafin ranar zaɓe.

Hukumar ta ƙara da cewa duk jam’iyyar da wannan buƙatar ta same ta sannan ta kasa cika sharaɗɗun da aka gindaya, to fa ba za a saurare ta ba bayan haka.

INEC ta ce ta wallafa sunayen ‘yan takarar da ta tantance a ofishinta na jiha da na ƙananan hukumomi a faɗin Jihar Ekiti, haɗe da shafinta na intanet da kuma shafukanta na sohiyal midiya don amfanin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *