Kisan biri ba sai da igwa ba

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ina fatan kowa yana lafiya musamman ma’abota wannan shafi na ALƘIBLA da ke zuwa duk mako. Taken wannan rubutun kamar yadda ya ke a sama wato ‘kisan biri ba sai da igwa ba’ zai iya sa ma’abota sauraron waƙoƙin gargajiya su fahimci inda na dosa wato waƙar marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina ga direba Ummaru Ɗanɗan Duna na Gwandu.

Dalilin kowa labarin a fili ya ke shi ne rasuwar Alhaji Ummarun da ke zaune a Kano shekara da shekaru. Shafukan yada zumunta na mutan Arewa masu nazartar waƙa da lamuran al’adun da su ka shafi yankin sun yi ta kawo tarihi da ma wata hira da a ka yi da marigayin. Gaskiya duk wanda ya samu marigayi Dakta Mamman Shata ya waƙe ba ya buƙatar wata gwagwarmayar neman suna ko a san da zaman mutum a birane da ƙauyuka inda a ke amfani da harshen Hausa.

Kazalika wannan wama na daga manyan waƙoƙin Dakta Shata wato ta Ummaru Dandan Duna don a cikin ta ne na zaƙulo taken rubutun inda ya ke buƙatar Ummaru da ya ɗauki mataki daidai gwargwado wajen gamawa da abokan gasar sa ko ma wataƙila waɗanda ke ma sa hassada a harkar tuƙi, Shata ya ba cew, “…Ɗau gora tittiƙe abun ka, kisan biri ba sai da Igwa ba.” Ka ga wannan ya nuna in mutum zai tafi fagen daga akwai irin makamin da ya kamata ya ɗauka bisa la’akari da nau’in yaƙin da ya tunkara.

Dakta Shata na ganin indai matsayin waɗanda za a yaƙa bai fi ƙarfin biri ba, to ba ma buƙatar amfani da manyan makamai irin igwa ko a ce bindiga, wannan yaƙi bai fi ƙarfin mutum ya ɗau sanda ko gora ya rarraɗe abokin adawa ba. In mai irin wannan yaƙi ya fito da takobi ka ya wuce gona da iri. Tsarin makamin da ke hannun mutum a nau’in yaƙi na nuna irin sanin ya kamatar sa da jarumtakar sa. Za ka ga an zo kokawa ko faɗa da makami amma sai ka ga mafi jarumta ya buƙaci a ajiye makamin a zo a nuna ƙarfin damtse wajen faɗan.

Domin fa makami kari ne a kan arangamar da za a yi. Ma’ana ai ba sai mutum ya kai ka ƙarfin damtse zai iya gamawa da kai in ya na riƙe da bindiga ba. Sau na wa mutane ‘yan ƙalilan za su auka wani gari su sanya mutane shigowa ƙarƙashin gado don su na riƙe da bindiga. A wata waƙa Dakta Mamman Shata mai amshin ‘Hakanan ne’ Dakta Mamman Shata ya yi kirarin cewa, “bindiga mai sa maza su kwankwanta..” illar da bindiga ke yi ta sa ka hukumomi ke hana mallakar bindiga barkatai da ma hana shigowar makamai barkatai don haka ba na jin akwai wani shago a kasuwannin mu da a ke sayar da bindiga a fili sai dai a ɓoye kuma in an gano mai saye da sayarwa za su shiga magana.

Mu dawo kan wannan waƙa da Mamman Shata ya ke ji da ita kuma ta yi tambari a kafafen labaru alal misali a zaven rana na rediyon tarayyar Nijeriya na Kaduna. Kalmomin da a ka yi amfani da su wajen waƙar na cike da zuga, kambamawa da kwarjantawa ta garzaya in mun saurari inda Shata ke cewa “Sai daji yai dameji” Ummaru kan shiga yayin da sauran direbobi kan rufa ma sa baya. Wato kamar a zamanin yau a ce ga ɓarayi a hanya, duk wanda ya samu labari da wuri zai dakata sai in lamarin ya lafa kafin ya cigaba da tafiya.

A tsarin yabon waƙar Dakta Shata ya ce in Ummaru ya samu wannan yanayi ya kan shiga gaba ya murƙushe duk miyagun iri a kan hanya don sauran mutane ko direbobi su wuce lami lafiya. Wani sashin waƙar na nuna tausayi da juayi don Shata na nuna duk lokacin da Ummaru ba ya gari bisa ma’ana idan ka na da wani mai tallafa ma ka, ya zama zai yi balaguro to ya kamata ya bar ma ka ɗan kasafi da za ka yi amfani da shi har ya dawo don kar ka zauna cikin hamma a yanayin da sauran mutane ba za su kawo ma ka ɗauki ba.

Cikin hikimar waƙa ta Shata duk da shi ke taimakon Ummaru sai ya ce “in tafiyar ba da ni za ka yi ba, Ummaru sai ka bar min kuɗin hura” don kar yunwa ta kassara ni kafin ka dawo yayin da mutane su ke ganin ni na ka ne don haka ba ni da matsala ko bai dace su tallafawa wanda ya yi tare da kai ba a matsayin ka na babbar giwa.

Hatta motar kan ta ta Ummaru, Dakta Shata ya zayyana ta da cewa, “mai tafiyar mesa a ka sai mai, gaban ta mota baya ko ko jirgi” ya cikata da cewa “jirgi ya nike hanya masa ku bi baya.” A gani na zayyana bayan motar da jirgi ba jirgin sama Shata ke nufi ba, jirgin qasa ne da dogon bayan motar ya ke kama da taragun jirgi. Duk da haka Dakta Shata a waƙar watarana da ya ke ya kan maimaita ta, ya ɗan damu tuntuɓen harshe wajen tausayawa matar rago. Shata na son ya ce matar rago don ya yi magana kan mijin ta da zai yiwu gwarzo Ummaru ya wuce a hanya sai ya ce “matar rago mu ka yi wa jaje ga ɗan ki can mun wuce shi a hanya..!”

Wannan ya sa Shata bai ji daɗi ba sai ya fake da caji a waƙar ya na cewa, “ya sha karo da ɗan wan dawa Umar,” daga nan sai ya juyo ya gyara tuntuven harshen ya na haɗa matar rago da mijin ta uwar rago da ɗanta.

In da za mu kare gane Shata ba ya son ko ba ya raye ya bar mutane a dubu game da kalaman sa a waqa, akwai inda a waƙar ta Ummaru ya ce, “Ummaru in an aza ma ka kaya…” sai ya lura ka da masu sauraro su ɗauka ɗaukar kaya ne kamar yadda ɗan dako ya ke yi ya dago buhu ya lafta a bayan sa, don haka sai Shata ya yi ƙarin haske da cewa ” Ummaru in an yi ma ka lodi…” don a fahimci cewa lodi ne na babbar mota. Amshin da kiɗan waƙar duk na da qarfin sauti da kuzari ta yadda mai sauraro ba zai gaji da waƙar ba kuma zai samu nishaɗi da fahimtar daɗin kalmomin da a ka sarrafa da harshen Hausa da ga su da santi a kan harshe kuma ba su da wahalar furtawa.

Zan yi amfani da wannan dama wajen taya duniyar Hausawa ta’aziyyar rasuwar Ummaru Dandan Duna da ma marigayi Mahdi mai dogon zamani Dakta Mamman Shata Katsina.

Adabi na buƙatar waƙoƙi masu ma’ana da isar da saƙonni masu amfani ga mutan yanzu da ma waɗanda za su zo ko bayan mu kan mu mun shuɗe. Sanyin gwiwa da na kan samu shi ne in an rasa wane zai yi wuya a samu makwafin sa cikin sauƙi.

Kun ga Ummaru wasa shi a ka yi ko da matsayin gwanintar sa bai kai haka ba amma aƙalla an koyi wasu hikimomi da fasahar zance. In mun tuna da waqar Dakta Shata ta Hassan Sarkin Dogarai ai akwai abun da ya wuce hankali wajen kambamawa kamar inda ya ce, “na yi zaton Ifiritu ne na kwalba da ya ke fita” da kuma,” Hassan mutum huɗu da rabin mutum, in karya ne ke ku tambayi likitan kashi.”

Duk wannan kwatance kawai na zaiyanar zuciya ba abun da ido ke gani a zahiri ba. Ko ma dai me za a ce, ita ma waƙar Hassan ta sa Hassan ɗin ya yi fice da qara martaba kuma zai yi wuya a manta shi duk tsawon shekaru bayan rasuwarsa.