Hukumar Kwastom ta tara wa Gwamnatin Tarayya Naira Miliyan 500 a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar hana fasa ƙwauri ta Nijeriya, wato Nigeria Customs Service, reshen Jihar Katsina, ta tattara kuɗin haraji da su kai kimanin Naira milyan 500 a cikin watanni bakwai tun bayan da gwamnatin tarayya ta sanar da buɗe iyakokin ƙasar nan ciki hadda iyakar dake tsakanin ƙasashen Najeriya da jamhuriyyar Nijar dake ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Babban Kwantorola na hukumar a jihar Dalha Wada Cedi ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.

Chedi ya kuma bayyana cewar a cikin watanni bakwai an yi shige da fice na kaya da kuɗin su ya kai kimanin Naira Bilyan 5 a iyakar ta Najeriya da Nijar.

“Kawo yanzu hukumar Kwastam ta tara Naira Milyan 500 daga ranar da aka sake buɗe iyakar Jibiya, an kuma samu kaya da darajar su ta kai kimanin Naira Bilyan 5 da suka fita daga iyakar,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewar hukumar ta kama kayan da aka shigo da su ta haramtacciyar hanya da kuɗin dutinsu ya kai kimanin Naira 77,803,825.

Ya cigaba da cewa hukumar ta kama buhunan shinkafa mai nauyin kilogram 50 guda 302,Katon na taliyar waje 361,sai kuma Katon 30 na Kuskus ɗan ƙasar waje, katan 40 na Makaroni, sai kuma dilar gwanjo 10, buhunan Filawa guda 37 yar waje, sai kuma jarkokin man fetur mai ɗaukar lita 25 guda 122 da kuma gas ɗin girki 41 mai nauyin kilogram 50.

Chedi ya bayyana cewar sun sami wannan nasarar daga ranar da aka sake buɗe iyakokin ƙasar nan don cigaba da gudanar da huɗɗar kasuwanci ta halastacciyar hanya tsakanin ƙasashen Najeriya da Nijar.