Da safiyar Talata aka samu aukuwar gobara a kasuwar wadda ta laƙume wani sashe na kasuwar.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewar gobarar ta tashi ne a sashen da galibi takalman mata ake sayarwa.
Da yake tabbatar da aukuwar iftila’in, hadimin Gwamnan Legas kan harkokin yaɗa labarai, Jubril Gawat, ya ce jami’an kwana-kwana sun dira kasuwar domin kashe gobarar.
Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, babu ƙarin bayani a hukumance game da abin da ya haddasa gobarar da kuma asarar da aka tafka a dalilin gobara.