19
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A qarshen makon da ya gabata ne jami’an ‘yan sanda suka yi artabu da ‘yan bindiga a ƙauyen Gada da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu a jihar Zamfara, inda aka kashe da dama daga cikin ‘yan bindigar, wasu da dama kuma suka gudu da harbin bindiga. ‘Yan bindigar ɗauke da muggan makamai sun hau babura da dama, inda suka mamaye al’ummar Gada, inda suka kashe mutanen yankin 8 tare da yin awon gaba da shanu da dama. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya ce sun samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar, kuma…
