Editor

9513 Posts
NNPP da LP sun bayyana matsayarsu kan APC

NNPP da LP sun bayyana matsayarsu kan APC

…Bayan Atiku ya nemi a yi wa jam’iyyar taron dangi*Ko a jikinmu, cewar APC Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar LP ta bayyana ƙudurin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, a matsayin shawara mai kyau da ya kamata a yi la’akari da ita. Sai dai ɗaya jam’iyyar adawa ta NNPP ta ce, za ta iya amincewa da ƙudurin ne kawai idan Atiku zai goyi bayan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, domin ya ƙwace mulki daga hannun jam’iyyar APC a 2027. Manyan jam’iyyun adawa na mayar da martani ne kan kiran da Atiku ya…
Read More
Shari’ar Gwamnan Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke nasarar Abba Gidada

Shari’ar Gwamnan Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke nasarar Abba Gidada

*Ta ce Abba bai cancanci tsayawa takara ba Daga BASHIR ISAH Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta bi sawun takwararta ta Sauraren Ƙararraki Zaɓen Kano wajen soke nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a zaɓen gwamnan jihar. A ranar 20 ga Satumba Kotun Sauraren Ƙararrakin ƙarƙashin jagorancin Alƙali Oluyemi Akintan Osadebay, ta soke nasarar Abba tare da bayyana Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe. Kotun ta yanke hukuncin haka ne bayan zabtare ƙuri'u 165,663 daga adadin ƙuri'un da Yusuf ya samu a zaɓen a matsayin ƙuri'u mara amfani kasancewar ba su ɗauke…
Read More
Hukumar Shari’a ta bada sunayen alƙalai 22 ga Kotun Ƙoli

Hukumar Shari’a ta bada sunayen alƙalai 22 ga Kotun Ƙoli

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An aika da jerin sunayen alƙalai 22 na Kotun Ɗaukaka Ƙara da Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Tarayya, FJSC, ta miqa sunayensu domin ɗaukaka darajarsu zuwa Kotun Ƙoli ga majalisar shari’a ta ƙasa, NJC. Blueprint Manhaja ta ruwaito sunayen waɗanda aka naɗa, waɗanda suka fito daga yankuna daban-daban na ƙasar, an bayyanasu a cikin takardar FJSC a ranar Alhamis. Yankin Arewa ta Tsakiya yana da mutum shida da aka zaɓa, yayin da shiyyar Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu ke da mutum biyu kowanne. Shi ma yankin Kudu maso Gabas yana da…
Read More
Ya za ta kaya a shari’ar zaɓen gwamnan Kano?

Ya za ta kaya a shari’ar zaɓen gwamnan Kano?

*Yau Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta yanke hukunci Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun Ɗaukaka Ƙara ta saka yau Juma'a, 17 ga Nuwamba, 2023, a matsayin ranar yanke hukunci kan ƙarar da Gwamnan Jihar Kano ya ɗaukaka, inda yake ƙalubalantar soke nasarar zaɓensa da kotun zaɓen jihar ta yi kwanakin baya. Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya garzaya gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ne bayan kotun ƙorafin zave ta Jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba ta rushe nasarar da ya samu a babban zaɓen 2023, inda ta ce abokin takararsa na Jam'iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna, ne halastaccen…
Read More
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce zaɓen gwamnan Zamfara bai kammala ba

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce zaɓen gwamnan Zamfara bai kammala ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan Jihar Zamfara, a matsayin wanda ‘bai kammala ba’. A hukuncin da ɗaukacin alƙalanta uku ƙarƙashin Mai shari'a Sybil Nwaka suka amince da shi, kotun ta soke halascin zaɓen Gwamna Dauda Lawal Dare na ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023. Kotun da yammacin ranar Alhamis a Abuja, ta kuma bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomin Zamfara uku, da suka haɗa da Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukkuyum. Ta ce, kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Jihar Zamfara, ba ta yi la’akari…
Read More
Na gaji fasahar rubutu daga mahaifiyata – Khairat U.P

Na gaji fasahar rubutu daga mahaifiyata – Khairat U.P

"Rubutu ba ruwansa da girman ka ko ƙanƙantarka" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Akwai masu ganin cewa ba a gadon basira ko wata baiwa ta ƙirƙira, domin kuwa wannan kyauta ce ta Allah. Amma fa duk da haka da akwai waɗanda za a iya cewa ƴan na gada ne da sun wuce ƴan na koya. Ummulkhairi Sani Panisau da aka fi sani da Khairat UP na daga cikin marubutan da suka taso cikin gidan rubutu, domin kuwa ƴa ce a wajen fitacciyar marubuciyar nan Sadiya Garba Yakasai, wacce ta rubuta littattafai fiye da 80, kuma har yanzu tana jan zarenta a…
Read More
Kuɗin namiji ba shi ne ya kamata mace ta yi tinƙaho da shi ba – Raihan Ƙamshi

Kuɗin namiji ba shi ne ya kamata mace ta yi tinƙaho da shi ba – Raihan Ƙamshi

"Idan har kasuwanci ka ke son yi sosai, sai ka soke bayar da bashi" DAGA MUKHTAR YAKUBU A yanzu dai za a iya cewa mata sun farka daga zaman rashin sana'a da a ke ganin an bar su a baya musamman a Ƙasar Hausa ta yadda a baya a ke yi wa matan yankin kallon koma baya a fagen kasuwanci da dana'a. Raihan Imam Ahmad wadda aka fi sani da Raihan Imam (Ƙamshi) ta na ɗaya daga cikin matasan mata da suke gudanar da harkokin kasuwancin su, kuma a yanzu ta kai matakin zama babbar 'yar kasuwa a vangaren kayayyakin…
Read More
Yadda za mu inganta sana’armu don yaƙi da talauci

Yadda za mu inganta sana’armu don yaƙi da talauci

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Kamar da wasa aka fara sanya hotunan kayan sayarwa da sana'o'i a zaurukan sada zumunta, ana aikawa da wanda aka saya, bayan an biya kuɗin ta banki, a motocin haya ko ta hannun wasu amintattu, yanzu wannan hanyar tallata kasuwanci ta zama babbar harka da miliyoyin ’yan kasuwa maza da mata ke samun kuɗaɗe masu yawa da abin rufin asiri. Da dama daga cikin waɗanda suke wannan kasuwanci ko dillanci, basu da rumfa ko shago, a gida suke ajiye kayansu, sai an saya sannan su fitar da shi zuwa tasha. Wasu kuwa ma ba su…
Read More
NLC, TUC sun dakatar da yajin aiki

NLC, TUC sun dakatar da yajin aiki

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) da Ƙungiyar 'Yan Kasuwa ta Nijeriya (TUC) da sauran takwarorinsu, sun dakatar da yajin aikin da suka fara tun ran 14 gs Nuwamban 2023. Dakatar da yajin aikin ya biyo bayan ganawar da ƙungiyoyin suka yi da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Lamarin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu. Taron wanda ya gudana a ofishin NSA ya samu halartar Shugaban TUC, Festus Osifo; Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja; Ministan Ƙwadago, Simon Lalong da sauransu. NLC ta shiga yajin aiki ne don nuna rashin jin daɗinta kan dukan da aka yi ws shugabanta…
Read More
2024: Gwamnan Jigawa ya gabatar wa majalisa kasafin N298.14bn

2024: Gwamnan Jigawa ya gabatar wa majalisa kasafin N298.14bn

Daga ABUBAKAR MUHAMMAD TAHEER Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi Ɗan Modi, ya gabatar da kasafin shekarar 2024 ga 'yan majalisar dokokin jihar a ranar Talata. Namadi ya bayyana cewa kasafin na 2024, za a kashe Naira biliyan 111.98 wajen gudanar da ayyukan yau da kullum. Haka kuma, ya ce an ware kashi 59% cikin 100% wanda adadin sa ya kai Naira biliyan 175.42 domin gudanar da manyan ayyuka a faɗin jihar. Ya ƙara da cewa an yi nazari da taka-tsan-tsan wajen tsara kasafin duba da yadda Dalar Amurka take tashin gwauron zabbi da kuma farashin ɗanyen mai a kasuwannin…
Read More