Editor

9513 Posts
Da sana’ar sayar da soson wanka mu ke samun rufin asiri a Ogun – Alhaji Ya’u

Da sana’ar sayar da soson wanka mu ke samun rufin asiri a Ogun – Alhaji Ya’u

Daga DAUDA USMAN a Legas Wani ɗan kasuwa mai gudanar da harkokin kasuwancin sayar da sosan wanka wanda ake kiransa da suna Kakan a Jihar Ogun, Alhaji Ya'u Samaila, ya bayyna cewa, da wannan sana'ar su ke samun rufin asiri a Ogun. Alhaji Ya'u, wanda ya kasance ɗan asalin ƙaramar hukumar Samaila ne da ke cikin Jihar Kano mazaunin Ogun, kuma shugaban Ƙungiyar Masu Sana'ar Kasuwancin Sosan Wanka Kakan a garin Ibafo ta Ogun ya bayyana cewa, shi da sauran 'yan Kasuwa masu sana'ar kasuwancin sosan kakan a garin Ibafo su na ƙara samun nasarori a wajen gudanar da harkokin…
Read More
Za mu tabbatar da kwatar wa marasa ƙarfi ’yancin su – Hajiya Rabi Salisu

Za mu tabbatar da kwatar wa marasa ƙarfi ’yancin su – Hajiya Rabi Salisu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kwamishinar Jinƙai da Walwalar Al'umma ta Jihar Kaduna, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim (Garkuwar Marayun Zazzau), wata jajirtacciyar mace ce mai kishi, da tausayi, da son taimaka wa al'umma. Tsayuwar dakar da ta yi wajen aikin tallafa wa waɗanda aka zalunta, zawarawa da marayu ne ya sa ta kafa Gidauniyar Arrida, wacce a dalilin ta mata da matasa da yara marayu masu yawan gaske ne suka amfana, kuma rayuwarsu ta inganta, wanda a kuma dalilin hakan ya sa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya naɗa ta a matsayin kwamishinar jinƙai ta jihar. Wakilin Blueprint Manhaja, MAHDI…
Read More
Kotu ta yanke hukuncin kisa a kan ɗan sandan da ya kashe Bolanle Raheem a Legas

Kotu ta yanke hukuncin kisa a kan ɗan sandan da ya kashe Bolanle Raheem a Legas

Babbar Kotun Jihar Legas ta yanke wa ɗan sanda, ASP Drambi Vandi, hukuncin kisa bayan da ta same shi da laifin kashe lauyar nan, Mrs Omobolanle Raheem a Legas. A ranar Litinin Kotun mai zamanta a yankin Igbosere a Legas, ta ce dakataccen jami'in zai baƙunci lahira ne ta hanyar rataya. Aƙalin kotun, Ibironke Harrison, ya ce mai gabatar da ƙara, wato Gwamnatin Jihar Legas, ta gabatar wa kotun ƙwararan hujjojin da suka tabbatar da aikata laifin da ake zargin jami'in da shi. “Kotu ta sami wanda ke kare kansa da laifi guda ɗaya, wato kisa. Za a rataye ka…
Read More
Sunday Igboho ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe shekara biyu a gidan yarin Jamhuriyar Benin

Sunday Igboho ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe shekara biyu a gidan yarin Jamhuriyar Benin

An sako jagoran neman kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, bayan shafe shekara biyu yana tsare a gidan yarin ƙasar Benin. Igboho ya tabbatar da sakin nasa ne a shafinsa na Instagram inda ya wallafa cewa, “Sako ni daga Jamhuriyar Benin." Majiyarmu ta ce Igboho ya yaba wa waɗanda suka taka rawa wajen sako shi da aka yi, da suka haɗa da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da fitaccen marubucin nan, Wole Soyinka da Farfesa Banji Akintoye da Ayo Adebanjo da sauran sarakunan gargajiya. Idan dai ba a manta ba, a ranar 19 ga…
Read More
Gwamnatin Kano ta rufe asibiti mai ma’aikata biyu rak

Gwamnatin Kano ta rufe asibiti mai ma’aikata biyu rak

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani asibiti mai zaman kansa mai suna Choice Clinic, bayan da aka gano ma'aikata biyu rak asibitin ke da su, wato nas ɗaya da mai shara ɗaya. Majiyarmu ta ce wannan na zuwa ne bayan da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar (PHIMA) ta rufe asibitin Reach Clinic kan laifin saɓa dokokin aiki. Da yake jawabi jim kaɗan bayan rufe asibitin, Daraktan hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar (PHIMA), Farfesa Salisu Ibrahim Ahmad, ya ce sun samu asibitin Choice Clinic na zama a gini guda…
Read More
Oyedele ga ‘yan Nijeriya – Gara ma ku yi fatan kar matatun mai su yi aiki a Nijeriya

Oyedele ga ‘yan Nijeriya – Gara ma ku yi fatan kar matatun mai su yi aiki a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Ɗaya daga cikin mataimakan da Shugaba Tinubu ya naɗa, Mista Taiwo Oyedele ya gaya wa 'yan Nijeriya cewa, su yi fatan kar Allah ya sa matatun man fetur su yi aiki a Nijeriya. Shugaban kwamitin shugaban ƙasa na tsare-tsaren kuɗi da saita haraji My MistaTaiwo Oyedele, shi ya isar da wannan gargaɗi ga 'yan Nijeriya. Ya ƙara da cewa, da zarar matatun sun fara aiki, litar man Nijeriya sai ta kere ta ko'ina a duniya tsada. Oyedele ya yi wannan jawabi ne a taron murnar ranar samun 'yancin kan Nijeriya da aka gudanar a ranar Litinin…
Read More
Dandalin shawara: Mahaifiyar ƙawata ke nema na da lalata

Dandalin shawara: Mahaifiyar ƙawata ke nema na da lalata

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Mummyna Aysha Asas sannu da aiki. Ya ki ke. Fatan kina cikin jin daɗi. Na kira layinki ya fi a ƙirga don sanar da ke tawa damuwa saidai ba a ɗauka ba. Ni dai shekarata 17, kuma dan Allah kar ki yi min mummunar fahimta. Wallahi tun 'last year' mahaifiyar 'best friend' ɗita ta neme ni don mu yi les, kuma ta ja ra’ayina har sai da na amince da ita. Tun daga nan ta ke zuwa tana ɗauka ta duk lokacin da babu karatu, ko mu je 'hotel' ko ta kai ni wani gida. To…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Zamfara

Bayanai daga Jihar Zamfara sun ce mutum 10 sun mutu sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai kan wasu motoci a hanyar Magami zuwa Gusau a ranar Asabar. An ce yayin harin, mahara sun ƙona motoci guda uku kana sun yi awon gaba da wasu fasinjoji da dama. Manhaja ta kalato cewar harin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana a yankin Dogon Tsauni a daidai lokacin da motocin ke hanyarsu ta zuwa Gusau daga Magami. Jaridar Premium Times ta ce an kwashi waɗanda suka ji rauni yayin harin zuwa babbar asibitin…
Read More
Illar cusa ƙiyayya a tsakanin al’umma (1)

Illar cusa ƙiyayya a tsakanin al’umma (1)

Assalamu alaikum, da fatan muna lafiya. Allah Ya yi mana jagora, ilahi. Mu sani cewa, kowane mutum da Allah ya yi, ya yi shi da irin nasa tunanin, kowa da yadda yake kallon abu idan ya zo masa, kamar yadda yake kuma kowa da irin nasa ra’ayin. Wasu ana iya kawar da su daga kan ra’ayinsa mummuna ko kyakkyawa, wasu kam ba yadda za a yi a iya kawar da su daga ra’ayin da suka ginu a kai. Irin wannan ra’ayi da fahimta da Allah ya yi kowa tasa daban, shi ne ya kamata a ce kowa ya tsaya a…
Read More
Nijeriya a 63: Har yanzu akwai jan-aiki a gaba

Nijeriya a 63: Har yanzu akwai jan-aiki a gaba

Yayin da Nijeriya ke cika shekara 63 da samun ’yancin kai, abin takaici har yanzu ƙasar na fama da matsaloli da ɗimbin alƙawuran da ba a cika ba. Matsalar rashawa da cin hanci ne dai babban ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, al'amarin da ya haifar da kusan dukkannin matsalolin da 'yan ƙasar ke fama da su. Lokaci ya yi da za a sake yin nazari a kan hanyar da za a bi wajen samun ingantacciyar ƙasa ta dimokuraɗiyya da kuma tsara mafi kyawun hanyar cigaba. Wannan tafiya ta kasance mai wahala tun daga farko. Misali shekaru shida bayan samun ’yancin…
Read More