08
Oct
Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Na taɓa wani rubutu da daɗewa ina mai cewa duk Musulmin Nijeriya na jin harshen Larabci ko da kuwa basa iya magana kai tsaye da harshen. In mun duba yadda a kan ba da umurni da harshen ka ga sun yi abun da a ka faɗa za a iya amincewa cewa batun haka ya ke. Alaƙa da addini kasancewar da harshen a ke magana ya yi matuƙar taimakawa wajen fahimtar harshen. A sallar Juma’a liman zai ce “ƙuumuu ila salaatikum…” sai ka ga manya da yara duk sun miƙe don fahimtar abun da a ka…
