Editor

9513 Posts
Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan ‘yan Nijeriya 250 a Habasha

Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan ‘yan Nijeriya 250 a Habasha

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattijai ta matsa ƙaimi domin gudanar da bincike kan kashe-kashe da ɗaure ‘yan Nijeriya sama da 250 a ƙasar Habasha. Hakan ya biyo bayan wani ƙudiri mai taken, ‘Akwai buƙatar a gaggauta bincike kan kashe-kashen da aka yi wa ‘yan Nijeriya sama da 250 a ƙasar Habasha ba bisa ƙa’ida ba, wanda shugaban marasa rinjaye, Sanata Simon Mwadkwon, ɗan Jam’iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) mai wakiltar Filato ta Arewa, da Sanata Victor suka ɗauki nauyi. Da yake gabatar da ƙudirin, Mwadkwon ya buƙaci majalisar dattijai da ta umurci kwamitocin ƙasashen waje da su…
Read More
‘Yan Nijeriya na iya neman fasfo ta yanar gizo daga watan Disamba

‘Yan Nijeriya na iya neman fasfo ta yanar gizo daga watan Disamba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce ana ci gaba da sauye-sauye domin sauƙaƙa aikin fasfo tare da yiyuwar 'yan Nijeriya su fara gabatar da aikace-aikacen samum fasfo ɗin ta yanar gizo tun daga watan Disamba. Da yake magana a gidan talabijin na Channels Television a shirin 'Siyasa A Yau' a Laraba, Tunji-Ojo ya bayyana cewa, ɗaya daga cikin sauye-sauyen da ma'aikatar ke aiwatarwa a fannin sarrafa fasfo shi ne kawo ƙarshen tsarin neman fasfo cikin wahala. “Ni da kaina na faɗi haka ga masu samar da ayyukan; Na faɗa yau, na fadi…
Read More
Gwamna Lawal ya karɓi baƙuncin ahalin da ayyukan ‘yan ta’adda suka jefa cikin mawuyacin hali a Zamfara

Gwamna Lawal ya karɓi baƙuncin ahalin da ayyukan ‘yan ta’adda suka jefa cikin mawuyacin hali a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya karɓi baƙuncin matar nan Hauwa'u tare da 'ya'yanta wanda ayyukan 'yan bindiga suka jefa cikin mawuyacin hali a jihar. Cikin wani faifan bidiyon da aka yaɗa kwanan nan, an ga yadda Hauwa'u tare da 'ya'yanta suna cin ciyawa a matsayin abinci don tsira da rayuwarsu. Mai magana da yawun Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya faɗa a ranar Alhamis cewa, halin da matar da 'ya'yanta suka tsinci kansu ya nuna akwai buƙatar gaggawa wajen maganace silar faruwar hakan da kuma taimaka wa rayuwarsu. Ya ƙara da cewa, baƙuncin matar da 'ya'yanta da Gwamnan…
Read More
Mutuwar Farfesa Umar Shehu babban rashi ne ga Arewacin Nijeriya – Gwamnonin Arewa

Mutuwar Farfesa Umar Shehu babban rashi ne ga Arewacin Nijeriya – Gwamnonin Arewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta yi alhinin rasuwar Emeritus Farfesa Umaru Shehu, Farfesan Farfesa na kiwon lafiyar al’umma na Arewacin Nijeriya, ya rasu ranar Litinin yana da shekaru 97 a duniya. Gwamnan jihar Gombe kuma shugaban ƙungiyar, Muhammadu Inuwa Yahaya, a cikin saƙon ta’aziyyarsa, ya bayyana Marigayi Umaru Shehu a matsayin haziƙi kuma ƙwararre na gaskiya wanda rasuwarsa ta haifar da gurbi mai tarin yawa a fagen ilimi da shugabanci a Nijeriya. A cewar Gwamna Yahaya rashin Farfesa Emeritus Umaru Shehu ya haifar da babbar matsala, ba wai ga iyalansa, jihar Borno da Jami’ar Maiduguri…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin Jami’ar Ɗanfodiyo a Sakkwato

Yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin Jami’ar Ɗanfodiyo a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mako guda bayan da 'yan bindinga suka sace ɗaliban Jami'ar Gwamanatin Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, a cikin daren ranar Litinin wasu 'yan bindiga sun kutsa Jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato suna harbe-harbe, inda suka yi awon gaba da kayan abinci da wasu kayayyakin amfani. Maharan sun kutsa jami'ar ne da misalin ƙarfe goma na dare inda suka shiga kasuwar da ke cikin jami'ar suna harbi a iska, abin da ya tayar da hankalin masu shaguna da sauran jama'ar da ke cikin kasuwar kuma kowa ya yi ta kansa. Shugaban Jami'ar…
Read More
Kada ku bari ƙa’idoji su hana ku yin adalci – Alƙalin Alƙalai ga alƙalan Nijeriya

Kada ku bari ƙa’idoji su hana ku yin adalci – Alƙalin Alƙalai ga alƙalan Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya gargaɗi alƙalan da su guji ƙyale wasu abubuwa su na kawo cikas wajen gudanar da shari’a. Ya kuma ce a matsayinsa na mai sasantawa tsakanin jam’iyyu, ɓangaren shari’a na ci gaba da yin abin da ake buƙata wajen sauke nauyin da ke wuyansu. CJN ɗin ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a wurin taron kara wa juna sani na ƙara ƙarfin alƙalai na Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) karo na 5 a Abuja. Kalaman na CJN ya zo ne a daidai…
Read More
Rasuwar Jaruma Binta Ola: Ba rabo da gwana ba…

Rasuwar Jaruma Binta Ola: Ba rabo da gwana ba…

Daga UMAR GARBA, a Katsina A ranar 3 ga Oktobo, 2023, Allah ya karɓi rayuwar shahararriyar jarumar Kannywood kuma ɗaya daga cikin mata da suka fara gudanar da wasan kwaikwayo a Arewacin Nijeriya, wato Hajiya Binta Suleiman, wadda aka fi sani da Hajiya Binta Ola Katsina. Marigayiya Hajiya Binta ta fara wasan kwaikwayo tun lokacin da ake wasan daɓe, wato kafin zuwan wasan kwaikwayo na talabijin da kuma fina finan zamani irinsu Kannywood.Wakilin Jaridar Blueprint Manhaja a Katsina, Umar Garba ya samu damar halartar gidan marigayiyar a Sabuwar Unguwa cikin garin Katsina inda iyalanta ke zaman ta'aziya. An haifi Hajiya Binta…
Read More
Nijeriya ta shirya ƙarfafa ƙawance da EU don yaƙi da matsalolin tsaro

Nijeriya ta shirya ƙarfafa ƙawance da EU don yaƙi da matsalolin tsaro

Ministan Tsaro Mohammed Badaru, ya bayyana cewa a shirye Nijeriya take ta ƙarfafa ƙawance da Ƙungiyar Ƙasashen Turai (EU) a fannin tsaro. Badaru ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar a ofishinsa da ke Abuja. Ya ce “Nijeriya na so ta farfaɗo da ƙawancenta da EU da ƙarfafa dangantaka wajen yaƙi da matsalolin tsaro. Ya ce lallai Nijeriya na da buƙatar samun kayayyakin aikin tsaro daga ƙungiyar EU don yaƙi da ƙalubalen tsaro a ƙasar. A cewarsa, “Manyan matsalolin tsaron da Nijeriya ke fuskanta su ne fashin fadaji a Arewa maso Yamma da Arewa ta…
Read More
’Yan wasan Al-Ittihad sun ƙi buga wasa saboda ajiye mutum-mutumi a ƙofar filin wasa

’Yan wasan Al-Ittihad sun ƙi buga wasa saboda ajiye mutum-mutumi a ƙofar filin wasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An ɗage wasan ƙwallon ƙafar da aka shirya bugawa a ranar Litinin tsakanin ƙungiyoyin Saudiyya da Iran a gasar cin Kofin Zakarun Nahiyar Asiya, sakamakon ajiye mutum-mutumin tsohon babban kwamanda a rundunar sojin ƙasar Iran Manjo Janar Qassem Soleimani a ƙofar filin da za a fafata wasan. Har zuwa wannan lokacin dai ba a sanya lokacin da za a kara tsakanin ƙungiyar Al Ittihad ta Saudiyya da Sepahan ta Iran ba, bayan da tawagar ’yan wasan Saudiya ta ƙi shiga filin da ke birnin Isfahan, saboda mutum-mutumin na marigayi Solaimani da aka ajiye a ƙofar shiga…
Read More
Rukunin farko na dakarun Faransa sun fara ficewa daga Nijar

Rukunin farko na dakarun Faransa sun fara ficewa daga Nijar

A jiya Alhamis, dakarun Faransa suka fara janyewa daga Jamhuriyar Nijar, kamar dai yadda shugaba Emmanuel Macron ya alƙawarta a ranar 24 ga watan Satumbar da ya gabata. Sojojin Faransa na farko da suka fara ficewa a jiyan su ne dakaru 400 da ke a yankin Walam, daf da iyakar Nijar da Mali, kuma sun kasance suna aikin samar da tsaro ne ƙarƙashin wani shiri da aka yi wa take 'Operation Almahaou', wanda babbar manufarsa ita ce samar da tsaro a yankin Liptako. Waɗannan dakaru za su isa birnin Yamai ne ta ƙasa, amma hakan na buƙatar cikakken tsari da…
Read More