Editor

9513 Posts
Gidauniyar Yadudu ta gudanar da taron faɗakarwa karo na 12 kan illolin cutar hanta

Gidauniyar Yadudu ta gudanar da taron faɗakarwa karo na 12 kan illolin cutar hanta

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An gudanarda taron ƙarawa juna sani na shekara na Marigayi Kyaftin Isma'ila Auwalu Yadudu akan illolin cutar hanta ƙarƙashin waƙafin Gidauniyar Yadudu. Taron an gudanar da shi a ranar Lahadi a ɗakin taro na gidan Mambayya da ya samu halartar mutane da dama. Da yake bayani ga manema labarai shugaban kwamitin amintattu na Waƙafin Gidauniyar Yadudu. Farfesa Auwalu Hamisu Yadudu ya ce taron na yi wa jama'a bayani ne na wasu abubuwa dake tattare da cutar hanta don a faɗakar a jawo hankali akan abinda za a guda dake jawo cutar da kulawa da yin…
Read More
Raba wa ‘yan Nijeriya 25,000 ba zai yi wani tasiri ba – ACF

Raba wa ‘yan Nijeriya 25,000 ba zai yi wani tasiri ba – ACF

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Dattawan Arewacin Nijeriya, ACF ta bayyana matsayinta game da tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnatin ƙasar da kuma manyan ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC a ranar Litinin, lamarin da ya kai ga janye yajin aikin da suka shirya tsunduma a ranar Talata 3 ga watan Oktoba. Bayan wata doguwar tattaunawa tsakanin wakilan ƙungiyoyin da wakilan gwamnati, yanzu dai ɓangarorin biyun sun cimma matsaya wadda ta kai da dakatar da tsunduma yajin aikin nan da kwana 30 masu zuwa. Dama ƙungiyoyin sun yi shirin shiga yajin aikin ne saboda matsin…
Read More
Karamcin marubuta ne ya sa na zama marubuciya – Fadila Lamiɗo

Karamcin marubuta ne ya sa na zama marubuciya – Fadila Lamiɗo

"Ba ƙaramar asara masu satar fasaha ke jawo wa marubuta ba" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubutan Jihar Kaduna kamar na sauran jihohi na ba da gagarumar gudunmawa ga cigaban harkokin adabi. Kama daga matakin ƙungiyoyi har zuwa a ɗaiɗaiku, Jihar Kaduna ta kasance sahun gaba wajen ƙyanƙyashe jajirtattun marubuta, masu ƙwazo da basira wajen ƙirƙirar labarai da ayyukan adabi iri daban daban. Fadila Lamiɗo, ɗaya ce daga cikin irin waɗannan marubuta masu ƙwazo da himma, kuma tun fara rubutun ta a shekarar 2016 ta samu karɓuwa da shahara cikin lokaci ƙanƙani. Ta kasance daga cikin matasan marubuta na onlayin da…
Read More
Mai shirin zama minista ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da tantance shi

Mai shirin zama minista ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da tantance shi

Mai shirin zama Minista daga Kaduna, Balarabe Abbas Lawal, ya yanke jiki ya faɗi a gaban 'yan Majalisar Dattawa yayin da ake tsaka da tantance shi a ranar Laraba. Da fari Balarabe ya yi jawabi na mintoci da dama kafin daga bisani ya yanke jiki ya zube a ƙasa. An ga 'yan majalisar sun yi ca a kan Balarabe bayan da ya zube a ƙasa domin ba shi agajin gaggawa. Hakan ya faru ne bayan ya kammala jawabi yake kuma shirin fara amsa tambayoyin 'yan majalisar. Daga bisani, 'yan majalisar sun je taƙaiccen hutu kafin farfaɗowar Balarabe.
Read More
Tsaro: Gwamnan Zamfara ya kama hanyar samar da Rundunar Kare Garuruwa

Tsaro: Gwamnan Zamfara ya kama hanyar samar da Rundunar Kare Garuruwa

A matsayin ɓangare na ƙoƙarin da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ke yi na inganta tsaro a faɗin jiharsa, ya kafa wani kwamiti musamman da zai fara aiki don assasa Rundunar Kare Garuruwa, wato "Community Protection Guard" a Turance. Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a shafinsa na facebook a ranar Laraba. Ya ce, "Bayan kwashe awanni muna tattaunawa kan harkar tsaro, a yau na ƙaddamar da kwamitin da zai fara aiki don samar da Rundunar Kare Garuruwa (Community Protection Guard). "Wannan yana daga cikin shirinmu don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Jihar Zamfara. "Babban aikin wannan kwamiti…
Read More
‘Yan bindiga sun sace wasu ɗaliban jami’ar FUDMA a Katsina

‘Yan bindiga sun sace wasu ɗaliban jami’ar FUDMA a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu mutane ɗauke da bindigogi da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun sace ɗalibai mata biyar dake karatu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsinma, wato FUDMA dake Jihar Katsina. 'Yan bindigar sun kutsa kai a gidan da ɗaliban ke kwana wanda ke wajen jami'ar bayan makarantar Mariamoh Ajiri dake garin na Dutsinma. Majiyar Manhaja ta ce 'yan bindigar sun yi dirar mikiya a rukunin gidajen da ɗaliban suka kama haya da misalin karfe 2:30 na safiyar Talata zuwa wayewar garin Laraba. Kakakin Rundunar 'Yan Sanda na jihar Katsina, ASP Sadiq Abubakar ya tabbatar da…
Read More
Gwamnan Kano ya nemi al’umma a dage da addu’ar zaman lafiya

Gwamnan Kano ya nemi al’umma a dage da addu’ar zaman lafiya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci al'ummar jihar da su dage da addu’ar samun zaman lafiya ga Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya. Ya yi wannan kira ne a cikin saƙon taya murnar bikin maulidin Fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) na bana wanda ya isar ta bakin Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta jihar, Baba Halilu Dantiye, MON wanda ka raba wa manema labarai a jihar. Albarkacin bikin maulidin na bana, Gwamnatin Jihar ta ayyana Laraba, 4 ga Oktoba, 2023 a matsayin ranar hutu domin tunawa da haihuwar fiyayyen…
Read More
Abubuwan nazari game da bukin murnar samun ‘yancin kai

Abubuwan nazari game da bukin murnar samun ‘yancin kai

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Shekara 63 kenan da samun ’yancin kan Nijeriya daga turawan mulkin mallaka. Kuma tun daga rana mai kamar ta yau wato ɗaya ga watan Oktoba na shekarar 1960 da turawan Ingila suka miƙa ragamar mulkin ƙasar nan ga shugabannin gwamnatin haɗaka ƙarƙashin jagorancin Firaminista Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, 'yan ƙasa ke shirya bukukuwa don raya wannan rana, da bayyana farincikinsu da jin daɗi na samun ’yanci da damar tafiyar da dukkan harkokin da suka shafi al'ummar Nijeriya, ba tare da neman amincewar Sarauniya ko Razdan ba. Turawan mulkin mallaka sun shafe tsawon shekaru suna bautar…
Read More
Da me matan banza suka fi na gida? (2)

Da me matan banza suka fi na gida? (2)

Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinmu na zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A makon da ya gabata mun kawo muku maudu'i kan mai matan bariki suka fi matan aure har wasu mazan suke tsallake matansu na aure suna biye wa 'yan bariki? Mun fara kawo muku dalilai har guda 7. A yanzu za mu ɗora daga inda muka tsaya. A sha karatu lafiya. Iya abinci: Matan wajen suna bai wa mazansu abinci. Wata ma a nan take wanke masa duk wani laƙani don mallake shi. Za ka ji namiji yana zancen abincin budurwarsa kamar…
Read More
Janar Musa ya nemi Ma’aikatar Kasafi ta bai wa ayyukan tsaro muhimmanci

Janar Musa ya nemi Ma’aikatar Kasafi ta bai wa ayyukan tsaro muhimmanci

Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, ya nemi Ma'aikatar Kasafi da Tsare-tsare da ta bai wa ayyukan tsaro muhimmanci. Janar Musa ya bauƙaci hakan ne yayin ziyarar aiki da ya kai wa Ministan Kasafi da Tsare-tsare, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ranar Talata a ofishinsa da ke Abuja. Cikin sanarwar da ta samu sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar tsaro, Tukur Gusau, Musa ya nemi Ma'aikatar da ta ware wa rundunar sojoji kaso na musamman domin aiwatar da wasu muhimman ayyuka da suka haɗa da samar da ƙarin gidaje ga sojoji da sauransu. Daga nan Janar ɗin ya bai…
Read More