04
Oct
Daga UMAR GARBA a Katsina Allah Ya yi wa shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, Hajiya Binta Ola rasuwa. Hajiya Binta ta rasu ne da misalin ƙarfe 3 na daren jiya Talata, a gidanta dake Sabuwar unguwa Ƙofar Ƙaura, dake jihar Katsina bayan gajeruwar rashin lafiya. Majiyar mu ta ce za a yi jana'izar marigayiyar a wannan Laraba da misalin ƙarfe 10 na safe a gidanta dake Sabuwar unguwa cikin garin Katsina.
