03
Oct
Jami'an DSS a Kano sun cafke Fiddausi Ahmadu, 'yar shekara 23, bayan da ta yi barazanar ƙunar baƙin-wake a kan waɗanda ta ce suna da hannu a nasarar da Jam'iyyar APC ta samu a shari'ar zaɓen gwamnan Kano a Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe. Majiya mai tsushe ta tabbatar wa jaridar News Point Nigeria da batun kama budurwar da DSS ta yi da safiyar Talata. Majiyar ta ce Fiddausi na iƙirarin taya Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusu da jam'iyyarsa ta NNPP faɗa ne kamar yadda aka gani a cikin wani faifan bidiyon da aka yaɗa. An ji Fiddausi a cikin bidiyon…
