Editor

9513 Posts
Gwamnatin Kano ta amince da naɗin kwamitin riƙo na ƙungiyar Kano Pillars

Gwamnatin Kano ta amince da naɗin kwamitin riƙo na ƙungiyar Kano Pillars

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin kwamitin riƙo na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars (Sai Masu Gida). A cewar sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ta ce, gwamnati ta naɗa shugaban hukumar da mambobi da sakatare da suka haɗa da: Babangida Little, Shugaba Garba Umar, Member Naziru Aminu Abubakar, memba Bashir Chilla, memba Ali Nayara Mai Samba, memba Shuaibu Ibrahim Doguwa, memba Rabiu Pele, memba Muhammed Danjuma, memba Sabo Chokalinka, memba Abba Haruna (Dala FM), mamba Engr. Usman Kofar Na’isa Yakubu…
Read More
Gwamnan Kano ya miƙa sunayen kwamishinoni ga majalisar jihar

Gwamnan Kano ya miƙa sunayen kwamishinoni ga majalisar jihar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane 19 da yake son ya naɗa a matsayin kwamishinoni a majalisar zartarwar jihar. A ranar Talata ce Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Honorabul Yusuf Falgore, ya karanto jerin sunayen da gwamnan ya aike wa majalisar. Waɗanda aka zaɓa ɗin dai za su hallara gobe Laraba da ƙarfe 10:00 na safe a gaban majalisar dokokin domin tantancewa. Ga jerin sunayen kamar haka: Comrade Aminu Abdulsalam Hon. Umar Doguwa Ali Haruna Makoda Hon. Abubakar Labaran Yusuf Hon. Danjuma Mahmoud Hon. Musa Shanono Hon. Abbas Sani Abbas Haj. Aisha…
Read More
Gwamnan Kaduna ya bai wa tsohon ma’aikacin Jaridar Blueprint muƙami

Gwamnan Kaduna ya bai wa tsohon ma’aikacin Jaridar Blueprint muƙami

Daga BASHIR ISAH Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya naɗa tsohon ma'aikacin Jaridar Blueprint, Samuel Aruwan, a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Birnin Kaduna (KCTA). Aruwan, wanda ya kasance Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna a baya-bayan nan, tsohon wakilin Jaridar Blueprint ne a jihar kafin daga bisani ya zama shugaban ofishin jaridar na Kaduna. Masanin aikin jarida ne wanda ke da ƙwarewar aiki na shekaru da dama inda a shekarar 2015 ya koma aiki da gwamnati. Sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya fitar a ranar Talata yaba da ƙwarewar Aruwan…
Read More
Yadda mutuwar mawaƙi Mahmud Nadanko ta girgiza al’umma

Yadda mutuwar mawaƙi Mahmud Nadanko ta girgiza al’umma

Daga AISHA ASAS A safiyar Lahadin da ta gaba ta ne, aka tashi da mummun labarin rashin ɗaya daga cikin 'ya'yan masana'atar finafinai ta Kannywood, jarumin barkwanci kuma mawaƙi, Mahmud Nadanko, wanda ya haɗu da ajalinsa a kan hanyarsa ta zuwa Jihar Kano tare da ƙaninshi da kuma mai ɗakinsa da ke tare da jaririn ɗansu. Wani abin tausayi da jan hankali ga mai rabo, wanda zai ƙara wa mai rabon shirya imani ya ƙara tabbatar da ba mai kashewa ko rayawa ba ya ga Allah shi ne, mai ɗakin tasa da ke tare da jinjirin ɗan mawaƙin, majiya mai…
Read More
An rantsar da sabbin alƙalan Kotun Ma’aikata shida

An rantsar da sabbin alƙalan Kotun Ma’aikata shida

Daga NASHIR ISAH A wani mataki na ƙarfafa ɓangaren shari'a na ƙasa, Alƙalin-alƙalai na Nijeriya (CJN), Mai Shari'a Olukayode Ariwoola, ya rantsar da wasu alƙalai sabbin ɗauka su shida na Kotun Ma'aikata. Rantsarwar ta gudana ne a Kotun Ƙolin da ke Abuja a ranar Litinin. Yayin rantsarwar, Mai Shari'a Ariwoola ya yi kira ga sabbin alƙalan da su yi aikin da ya rataya a kansu bilhaƙƙi da kuma martabawa daidai da tanadin dokar ƙasa. Ya ƙara da cewa, ɓangaren shari'ar ƙasar nan na buƙatar maza da mata masu nagarta waɗanda za su kwatanta gaskiya ga 'yan ƙasa ba tare da…
Read More
Yadda MOPPAN ta bunƙasa ƙarƙashin Dr Sarari

Yadda MOPPAN ta bunƙasa ƙarƙashin Dr Sarari

Daga AISHA ASAS A ranar Asabar 10 ga Yunin 2023 ne ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa ta gudanar da taronta na ƙarshen shekara, inda ta gayyaci dukkanin shugabanni a matakin ƙasa da jihohi. Taron, wanda ya gudana a babban zauren taro na Kannywoo TV da ke Tudun Yola a cikin birnin Kano, ya kafa babban tarihi a masana’antar shirya finafinan Hausa. Babban abin da ya fi ba wa mahalarta taron sha’wa, ciki, har da wakilan kwamitin Amintattu da na kwamitin ayyuka na musamman da tsare-tsare, shi ne yadda Shugaban qungiyar Dr. Ahmad Muhammad Sarari ya ɗauki lokaci wajen bayyana ayyukan ci…
Read More
Tsohon Gwamnan Binuwai, Samuel Ottom ya amsa gayyatar EFCC

Tsohon Gwamnan Binuwai, Samuel Ottom ya amsa gayyatar EFCC

Tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya amsa gayyatar Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Ta'annati (EFCC). A ranar Talata EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan don amsa mata tambayoyi kan abin da ya shafi zamanin mulkinsa. Majiyarmu ta ce Ortom ya isa harabar ofishin hukumar da ke Makurdi ne da misalin ƙarfe 10:08 na safe. Ƙarin bayani na tafe...
Read More
Tinubu zai yi ziyarar aiki ta farko tun bayan kama mulki

Tinubu zai yi ziyarar aiki ta farko tun bayan kama mulki

Daga BASHIR ISAH Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tafi ziyarar aiki Paris, babban birnin ƙasar Faransa ya zuwa ranar Alhamis, 22 ga Yuni. Wannan ita ce ziyara ta farko da Tinubu zai yi a matsayin Shugaban Ƙasa. Tinubu zai yi ziyarar ce domin halartar taron shugabannin duniya inda za su rattaɓa hannu kan Sabuwar Dokar Kuɗi ta Duniya wadda za ta da ba da fifiko kan ƙasashe marasa ƙarfi wajen samun tallafi da zuba jari biyo bayan matsanancin sauyin yanayi da kuma bayan tasirin annobar Korona. Taron wanda na yini biyu ne, zai gudana ne daga ranar 22 zuwa 23…
Read More
Tarihin shahararren marabucin Ƙasar Hausa, Alhaji Abubakar Imam

Tarihin shahararren marabucin Ƙasar Hausa, Alhaji Abubakar Imam

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dangane da adabin Hausa da adabin Arewacin Nijeriya, Alhaji Abubakar Imam na ɗaya daga cikin manyan marubutan da rubuce-rubucensu suka yi nuni da al’adun Arewa. Sai dai ba abun mamaki ba ne yadda ya fito daga jihar Neja, wadda daman jiha ce mai daɗaɗɗen tarihi na marubuta masu hazaƙa. Ya rubuta litattafai da dama da suka rayu har bayan rasuwarsa. Don fahimtarsa, mutum na buƙatar karanta ko wane shafi masu ban sha'awa na littattafansa don gane wa kansa wane ne Alhaji Abubakar Imam. Malami ne, mai kishin ganin al'ummarsa sun sami ilimi. Har ila yau, ya…
Read More
Bill Gates da Ɗangote sun jinjina wa Tinubu kan cire tallafin

Bill Gates da Ɗangote sun jinjina wa Tinubu kan cire tallafin

Daga BASHIR ISAH Hamshaƙin ɗan kasuwar nan Aliko Ɗangote da takwaransa Bill Gates da ya kasance Shugaban Bill and Melinda Gates Foundation, sun taya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu murnar cire tallafin man da ya yi haɗi da sauran nasarorin da ya samu ya zuwa yanzu. Ɗangote ya bayyana hakan ne a ganawar da ya yi da manema labaran Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan ganawarsu da Shugaba Tinubu a ofishinsa a ranar Litinin. A cewar Ɗangote, ana sa ran cire tallafin ya zama mabuɗi na hanyoyin samun ƙarin kuɗaɗe ga ƙasa don bai wa gwamnati zarafin zuba jari a sauran…
Read More