Editor

9513 Posts
A mayar da tsohon mataimakin gwamnan Zamfara Mahdi da aka tsige kujerarsa – Kotu

A mayar da tsohon mataimakin gwamnan Zamfara Mahdi da aka tsige kujerarsa – Kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada umarnin mayar da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara wanda aka tsige, wato Mahadi Aliyu Gusau kan kujerarsa. Mahadi dai shi ne Mataimakin Gwamna zamanin mulkin tsohon Gwamna Bello Matawalle, wanda aka tsige saboda ya ƙi bin shi Jam’iyyar APC daga PDP. Mahadi da PDP ne suka shigar da ƙarar suna ƙalubalantar tsige shi da Majalisar Dokokin Jihar ta yi a watan Fabrairun 2022. Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, Alƙalin kotun, Mai Shari’a Inyang ya ce matakin da tsohon Gwamna Matawalle da kwamitin…
Read More
Ronaldo ya kafa sabon tarihi a duniyar ƙwallon ƙafa

Ronaldo ya kafa sabon tarihi a duniyar ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kyaftin ɗin Portugal Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihin zama ɗan wasa na farko da ya buga wasannin ƙasa da ƙasa 200 a wasan neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Turai ta Euro 2024 da suka doke Iceland da ci 1-0. Ɗan wasan mai shekaru 38 shine ya ci ƙwallon da ta bai wa Purtgal nasara a mintuna na 89 ana daf da ƙarƙare wasa. Da farko alƙali ya zaci ƙwallon satar fage ce, amma na’urar VAR ya amince da cin lamarin da ya faranta wa Ronaldo a daren mai cike da tarihi. Wannan ita ce…
Read More
A baya akasarin manyan marubuta suna hantarar ƙanana masu tasowa – Gimbiya Amrah

A baya akasarin manyan marubuta suna hantarar ƙanana masu tasowa – Gimbiya Amrah

"Marubutan littafi da na onlayin gudunmawa ɗaya suke bayarwa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Gimbiya Amrah Auwal Mashi, fitacciyar marubuciyar online ce daga Jihar Katsina. Tana daga cikin matasan marubutan da suka ciri tuta, a fannin rubuce-rubucen almara da jarumta. Tun da ta rungumi alƙalami a shekarar 2014 har yau ba ta ajiye ba. Rubutu take yi babu kama hannun yaro, a ƙalla yanzu tana da littattafan da ta rubuta sun fi 20. A zantawarta da wakilin Manhaja Blueprint, Gimbiyar ta bayyana irin nasarorin da ta riqa samu a gasanni daban-daban, ciki har da Gasar Hikayata, Mu Gani A Ƙasa, da…
Read More
A fara koyon mulki da baki kafin a fara koyon mulki da hannu

A fara koyon mulki da baki kafin a fara koyon mulki da hannu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Yanzu dai kusan za a iya cewa, sabuwar gwamnati ta fara kankama sosai, yayin da ake cigaba da naɗe-naɗen masu dafa wa ayyukan gwamnati, da zaɓen shugabannin Majalisar Ƙasa zango na goma. ’Yan siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati sun yi rawar gani wajen tabbatar da cewa, waɗanda za a bai wa waɗannan muƙamai masu muhimmanci ba su ta fi a ɓangare guda ba. Babu ma kamar yadda aka riƙa qorafin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta Musulmi da Musulmi ce, saboda yadda gambizar Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa, ɗan Kudu da ɗan Arewa, duk suka zama…
Read More
Ilimin sana’a kafin fara ta na da matuƙar muhimmanci – Hauwa Garba Ilah

Ilimin sana’a kafin fara ta na da matuƙar muhimmanci – Hauwa Garba Ilah

"Ba sai ka rasa ba ne za ka yi sana'a" Daga AISHA ASAS Yanayin yadda mata matasa ke zage damtse wurin neman na kai don gujewa zaman kashe wando abin a yaba ne, a kuma jinjina wa ƙoƙarin su, ganin cewa, ba su bari ƙalubale da irin kallon da al'ummarsu ke yi masu ya sare masu gwiwa ba. Bincike ya nuna cewa, adadin mata da ke neman na kai a Ƙasar Hausa na gab da cimma adadin da ke zaman banza. Wannan kuwa ba ƙaramin cigaba ne a rayuwar mata, musamman ma bayan aure, kasancewar sana'a na taka muhimmiyar rawa…
Read More
An yi wa Shugaban Ƙasa da gwamnoni ƙarin albashi da kashi 114

An yi wa Shugaban Ƙasa da gwamnoni ƙarin albashi da kashi 114

Daga BASHIR ISAH Hukumar Tattara da Raba Kuɗaɗen Shiga (RMAFC), ta amince da ƙarin albashi da kashi 114 ga manyan jami'an gwamnati. Waɗanda ƙarin albashin ya shafa sun haɗa da Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa, gwamnoni, 'yan majalisu, ma'aikatan shari'a da sauransu. RMAFC ita ce hukumar da ke tantance albashin da ake yanka wa 'yan siyasa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa, ciki har da Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Gwamnoni da sauransu kamar yadda Sashe na 84 da 124 na Kundin Tsarin Mulki ya nuna. Shugaban RMAFC, Muhammadu Shehu, bisa wakilcin kwamishina a hukumar, Rakiya Tanko-Ayuba, shi ne ya…
Read More
Rusau: Saƙon kar-ta-kwana ga Gwanan Kano

Rusau: Saƙon kar-ta-kwana ga Gwanan Kano

Daga MUSBAHU BAFFA A Gwamnatance komai na tafiya ne da tsari bisa doron mu’amala da al'ummar da ake mulka. Yayin da duk aka rasa hakan tsakanin Gwabnati da al'umma, tabbas ba mulkarsu ake ba, bautar da su ake. Mai girma Gwabna, mun san cewa ana rushe gini domin sabuntawa ko kuma don kwaskwarima ko kuma sake fasali yayin da duk buƙatar hakan ta taso. Sai dai yana da kyau a fahimtar da al'ummar gari don su fahimta, domin suna da haƙƙin hakan. Mai girma Gwabna, tsohon Gwabnan Kaduna da ya gabata ya rushe gadar Kawo, inda ya sabuntata. Kuma tabbas…
Read More
N3m kacal na tarar a asusun Zamfara – Gwamna Dauda

N3m kacal na tarar a asusun Zamfara – Gwamna Dauda

'Da bashi nake gudanr da harkokin jihar' Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara,Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa, Naira miliyan uku kacal ya tarar a asusun jihar bayan da ya karɓi mulki ranar 29 ga mayu. Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a hirar da BBC Hausa ta yi da shi a ranar Litinin. Lawal ya ce gwamnatin da ya gada ta gaza biyan albashin ma'aikata na wata uku a jere kafin mulki ya dawo hannunsa. “Mummunan yanayi muka gada,” in ji Lawal. Ya ci gaba da cewa, “Gwamnatin da ta gabata ta bar asusun jihar a bushe babu komai.…
Read More
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Daga MUSBAHU BAFFA NA 'YAR TALLA (Bakwankwashe) Bayan gausuwa mai tarin yawa da fatan kana cikin ƙoshin lafiya. Tabbas zuwanka a matsayin Gwabnan Jahar Kano a irin wannan yanayin da Jahar ta samu kanta ba ƙaramar nasara ba ce ga al'ummar Jahar. Ka zo a gaɓar da aka cefanar da asibitin Yara na Hasiya Bayero akan kuɗi Naira Miliyan 6 kacal, duk kuwa da irin yadda al'ummar Jahar ke amfanuwa da shi. Ka zo a gavar da aka rushe Kotu guda ba tare da sanin Alƙalin Kotun ba, aka cefanar da gurin don gina Plaza. Ka zo a gaɓar da…
Read More
Rusau a Kano: Ƙungiya ta yi barazanar maka Gwamna Abba a kotu

Rusau a Kano: Ƙungiya ta yi barazanar maka Gwamna Abba a kotu

Ta bai wa Gwamnan sa'o'i 72 ya janye aikin rusau da yake yi Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Good Governance and Change Initiative (GGCI), ta bai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, wa'adin sa'o'i 72 a kan ya dakatar da rusau da yake yi a jihar sannan ya gayyato 'yan kasuwa da ɗaiɗaikun mutanen da lamarin ya shafa don warware matsalar cikin ruwan sanyi. Ƙungiyar ta yi barazanar maka Gwamnan a kotu muddin wa'adin da ta shata masa ya ƙare ba tare da yin abin da ya kamace shi ba. Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Talata…
Read More