20
Jun
Daga BASHIR ISAH Gwamna Duada Lawal na Jihar Zamfara, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da tagwayen hanyoyi a hanyar Gusau zuwa Funtua domin bunƙasa cigaban jihar. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Nuhu Salihu, ya fitar ranar Litinin a Gusau, babban birnin jihar. Gwamna Lawal ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki wa Babban Sakataren Ma'aikatar Ayyuka ta Tarayya, Mamuda Mamman, a ofishinsa. Ya ce hakan ɓangare ne na alƙauran da ya yi wa talakawansa a lokacin neman zaɓe. Ya ƙara da cewa, mayar da…
