Editor

9513 Posts
Mun san kyautata wa iyaye na kawo cigaba a rayuwa kuwa?

Mun san kyautata wa iyaye na kawo cigaba a rayuwa kuwa?

Assalamu alaikum, na fahimci cewa kamar wasunmu ba mu san muhimmancin kyautata wa iyaye ba, duba ga irin zamanin da muke ciki yanzu, mun mayar da iyayenmu tamkar ba komai ba. Misali, a irin unguwar da nake, wasu matasan za ka ga kamar sun fi ƙarfin iyayen su, domin iyayen ba su isa su gaya musu komai ba su ji, wanda kuma nike ganin hakan bai kamata ba. Mu sani fa cewa, idan mutum ba ya kyautata wa iyayen sa, duk abin da ya ke nema a rayuwa ba zai taɓa samu ba, zai rinƙa shan wahalar banza ne kawai…
Read More
Zuwa ga Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero

Zuwa ga Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero

Assalam alaikum. Bayan sallama da gaisuwa irin wacce a kan yi wa ma'abota kwanciyar kushewa, da fatan Allah ya juya kafaɗarka ya Rahamsheka. Dalilin rubuto maka wannan wasiƙa ita ce domin yin addu'a gareka da ambaton wasu kyawawan ayyukan da ka yi a lokacin rayuwarka wacce har ya zuwa yau muka kasa mantawa da kai, idanuwanmu ba su dai na zubar da hawaye ba, kuma tabon raunin da muka samu a sanadiyyar rashinka ya kasa warkewa. Allahu Akbar! Kwanci-tashi babu wuya, kamar jiya kabar doron duniyar nan, amma gashi muna ƙidaya shekaru tara cif-cif da rasuwarka. Ina son sanar da…
Read More
Sarkin Musulmi ya bayyana ranar Babbar Sallah

Sarkin Musulmi ya bayyana ranar Babbar Sallah

Daga BASHIR ISAH Ranar 28 ga watan Yuni idan Allah Ya kai mu take Babbar Sallah (Idil Kabir) ta bana. Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III ne ya bayyana haka ranar Lahadi da daddare biyo bayan ganin jinjirin watan Zul-Hajja. Sarkin Musulmi ya ce sakamakon ganin jinjirin watan, ya tabbata yau (Litinin) 1 ga Zul-Hijja na shekarar 1444 wanda ya yi daidai da 19 ga Yunin 2023. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Shugaban Kwamitin Bada Shawara na Fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya…
Read More
Ba zan zauna a PSG har ƙarshen 2024 ba – Mbappe

Ba zan zauna a PSG har ƙarshen 2024 ba – Mbappe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kylian Mbappe ya ce, ya sanar da ƙungiyar Paris St-Germain a cikin watan Yulin 2022 cewar ba zai zauna a ƙungiyar fiye da ƙarshen kakar 2024 ba. Yarjejeniyar ɗan wasan mai shekara 24 za ta ƙare a ƙarshen baɗi da cewar za a iya tsawaita masa shekara ɗaya. A baya ya aika wa ƙungiyar da wasiƙar cewar ba zai cigaba da buga wasa a ƙungiyar da zarar wa'adinsa ya cika a birnin Faris. Kenan PSG za ta yi shirin sayar da Mbappe a kakar nan, idan ba haka ba za ta yi asararsa a matakin wanda…
Read More
Sanusi ya yi ganawar sirri da Tinubu

Sanusi ya yi ganawar sirri da Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A jiya Alhamis ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da Sarkin Kano na 14 kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi (Khalifa Muhammadu Sanusi II), a fadar Aso Rock. Ziyarar ta Sanusi, wadda ita ce ta farko tun bayan da shugaban ƙasar ya hau karagar mulki, na zuwa ne mako guda bayan da shugaban ƙasar ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN. Ba a tantance tattaunawar da suka a wannan ganawa ta sirri ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto. Sanusi ya riƙe muƙamin shugaban CBN…
Read More
Tinubu ya amince da buƙatunmu har da N200,000 mafi ƙarancin albashi – TUC

Tinubu ya amince da buƙatunmu har da N200,000 mafi ƙarancin albashi – TUC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC, ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta shirya yi, inda ta danganta matakin da Gwamnatin Tarayya qarqashin jagorancin Bola Tinubu ta cimma cika dukkan buƙatunsu. Da farko dai ƙungiyoyin awadagon sun ƙaddamar da yajin aikin ne sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi, wanda hakan ya haifar da ƙarin farashin man fetur da tsadar rayuwa. Babban maƙasudin yajin aikin dai shi ne matsawa Gwamnatin Tarayya lamba kan ta sauya ƙarin kashi 200 cikin 100 na farashin man fetur. Bayan tattaunawa da yawa da suka haɗa da wakilai daga gwamnatin…
Read More
Hajjin 2023: Yadda ake jigilar mahajjata cikin hanzari

Hajjin 2023: Yadda ake jigilar mahajjata cikin hanzari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Matsaloli da kurakuran da suka gabata kamar wuƙa ne, ko dai ta yi mana amfani ko kuma ta yanke mu, kuma ya dogara ne da yadda muka riqeta ta hanyar wajen kaifin ko kuma ta hannun riƙewa. Ana ci gaba da jigilar Maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 cikin wasu ƙalubale nan da can. Saurin da hawan jirgin ke tafiya ya saɓa wa ƙarancin aiki da aka kawo na tsawon sa'o'i masu yawa, ta yin amfani da ƙaramin jirgin da wasu masu jigilar Alhazai da aka naɗa da…
Read More
Ƙaddamar da majalisa ta goma da ƙalubalen da ke gabanta

Ƙaddamar da majalisa ta goma da ƙalubalen da ke gabanta

A ranar 13 ga watan Juni, 2023, ne aka rantsar da Majalisar Dokokin Tarayya ta 10 a Abuja, tare da zaɓen sabon Shugaban Majalisar Dattajai da Kakakin Majalisar Wakilai bayan fafatawa mai zafi a takarar waɗannan muƙamai. A Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ne ya samu nasarar lashe zaɓen zama shugaban majalisar inda ya kayar da abokin takararsa Abdul'Azizi Yari. Nan ta ke kuma aka rantsar da shi. Sanata Ali Ndume na cikin waɗanda suka goyi bayan zaɓen Sanata Akpabio. Hakazalika, Honarabul Tajudeen Abbas wanda shi ne zaɓin jamiyyar APC, ya zama Kakakin Majalisar Wakilai ta 10. Majalisar Dokokin ta…
Read More
Umarnin Kotu: Ba mu hana Emefiele ganin iyali da lauyoyinsa ba – DSS

Umarnin Kotu: Ba mu hana Emefiele ganin iyali da lauyoyinsa ba – DSS

Daga BASHIR ISAH Hukumar tsaro ta DSS ta ce, an bai wa tsohon Gwmnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, damar ganin iyalinsa d likitocinsa tun kafin umarnin kotu a kan haka. Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa DSS umarni kan ta ƙyale Emefiele ya gana da iyalai da kuma lauyoyinsa. Sai dai cikin sanarwar da ta fitar ranar Asabar ta bakin kakakinta, Peter Afunanya, DSS ta ce ta rigaya ta bai wa tsohon Gwamnan na CBN damar ganawa da lauyoyin nasa tun kafin kotu ta ba da umarni. Sanarwar ta ƙara da cewa, DSS na…
Read More
Iyalan Nnamdi Kanu sun kori lauyoyinsa

Iyalan Nnamdi Kanu sun kori lauyoyinsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Iyalan Shugaban Ƙungiyar Masu Fafutukar Kafa Ƙasar Biyafara (IPOB) da ake tsare da shi, Mazi Nnamdi Kanu, sun kori manyan lauyoyinsa, Mike Ozekhome, SAN; da Ifeanyi Ejiofor. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aanin Kanu, Kanunta Kanu, ya fitar kuma ya wallafa a shafinsa na Tiwita a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2023. Zargin ƙin amincewa da lauyoyin suka yi na barin likitocin Kanu na ƙashin kansa su same shi domin yi masa tiyatar gaggawa ne babban dalilan ɗaukar matakin. Sanarwar mai taken ‘Sanarwar sallama’ a wani vangare tana cewa “Mik Ozekhome,…
Read More