18
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Majalisar Dattawa, Mista Godswill Akpabio, ya bayyana bayyana cewa, Majalisar Dokokin Nijeriya ta gamsu da ayyuka da matakan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka. Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawarsa da shugaban ƙasar. Ya ce, majalisar za ta haɗa hannu da vangaren zartarwa na gwamnati domin inganta rayuwar ’yan Nijeriya. “Shugaban ƙasa ya riga ya fara ayyuka, kawai yana buƙatar goyon bayanmu ne don cigaban ayyukan a ƙasa. Don haka, majalisar da za ta dawo…
