17
Jun
Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana cewa matasa suna da rawar da za su taka wajen cigaba da bunƙasa harkar kasuwanci a Jihar Kano. Alhaji Abdu Muhammad Aja, ɗaya daga cikin iyayen kasuwar Wapa ne ya bayyana hakan a lokacin da ake rantsarda sabbin zaɓaɓɓun ƙungiyar 'yan canji ta Al'amanat ta Wapa. Ya ce abin farin ciki shine sabon zaɓaɓɓen shugaban qungiyar Alhaji Sani Salisu Dada tun yana zagayen yaƙin zave ya ce yana neman taimakonsu a matsayinsu na iyayen ƙungiya da yayyen sa da sauran tsofaffin shugabanni. Ya fara da cewa in Allah ya so ya yarda zai…
