Editor

9513 Posts
Rikicin siyasa ya ci mutum uku a Kano

Rikicin siyasa ya ci mutum uku a Kano

Ana fargabar mutum uku sun mutu sakamakon rikicin zaɓe da ya ɓarke a yankin Ƙaramar Hukumar Wudil a Jihar Kano. Jaridar News Point Nigeria ta ce wasu 'yan daban siyasa ne suka kai hari rumfar zaɓe a yankin wanda hakan ya haifar da rikici yayin zaɓen na ranar Asabar da ta gabata. A cewar wani wanda lamarin ya faru a gabansa, rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku tare da ƙona gidaje aƙalla guda uku. Sai dai kuma, da aka nemi jin ta bakinsa Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano, Haruna Kiyawa, bai tabbatar da faruwar hakan ba. Ya ce…
Read More
Sakkwato ta Arewa: Sanata Wamakko ya yi ta-zarce

Sakkwato ta Arewa: Sanata Wamakko ya yi ta-zarce

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko na Jam'iyyar APC ya sake lashe zaɓen sanatan Sakkwato ta Arewa. Wamakko ya samu nasarar ce a zaɓen cike giɓin da INEC ta gudanar a ranar Asabar inda ya samu ƙuri'u 141,468. Abokin hamayyarsa na Jam'iyyar PDP, Dan’iya Manir Muhammad ne ya zama na biyu da ƙuri'a 118,445. Farfesa Ibrahim Magawata shi ne Baturen Zaɓen da ya bayyana sakamakon zaɓen da aka gudanar a rumfunan zaɓe 185.
Read More
Tambuwal ya sha da ƙyar a takarar Sanatan Sakkwato ta Kudu

Tambuwal ya sha da ƙyar a takarar Sanatan Sakkwato ta Kudu

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi nasarar lashe kujerar Sanatan Sakkwato ta Kudu da ya nema. Baturen zaɓen yankin, Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo, shi ne ya sanar da nasarar Tambuwal inda ya ce ya samu ƙuri'u 100,860 wanda hakan ya ba shi damar doke abokin karawarsa na APC, Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba wanda ya tsira da ƙuri'u 97,884. Nasarar Tambuwal ɗin dai na zuwa ne bayan da zaɓen kujerar ya kasance wanda bai kammalu ba a zaɓen yayin zaɓen 'yan Majalisar Tarayya da aka gudanar ran 18 ga watan Maris ɗin da ya…
Read More
Hedikwatar INEC ta ƙi amincewa da bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa

Hedikwatar INEC ta ƙi amincewa da bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa

*Ta ba da umarnin dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaɓe Babban Ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ya dakatar ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen cike giɓi na Gwamnan Jihar Adamawa da ya gudana ranar Asabar. Ofishin ya ɗauki wannan mataki ne bayan da labarin ayyana 'yar takarar Jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓe da Kwamishinan Zaɓe na jihar, Farfesa Hudu Yunus Ari, ya yi a ranar Lahadi ya isa gare shi. Cikin sanarwar da INEC ta wallafa a shafinta na Tiwita mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan hukumar, Barista Festus…
Read More
Sanata Binani ta ɗaɗa Gwamna Fintiri da ƙasa a Adamawa

Sanata Binani ta ɗaɗa Gwamna Fintiri da ƙasa a Adamawa

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ayyana Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa. Kwamshinan Zaɓe na Jihar Adamwa, Farfesa Hudu Yunus Ari, shi ne ya bayyana nasarar Binani wadda ta kasance 'yar takarar Jam'iyyar APC. Da fari, Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam'iyyar PDP ne ke gaba da yawan ƙuri'u kafin daga bisani Binani ta shige gabansa. Magoya bayan jam'iyyar PDP sun nuna rashin jin daɗinsu ganin Kwamishinan Zaɓe na jihar ne ya bayyana sakamakon zaɓen maimakon Baturen Zaɓe. Da wannan nasarar da ta samu, a iya cewa Sanata Aisha ta zamo mace ta…
Read More
Zaɓe: EFCC ta cika hannu da mutum 12 a Kano da Katsina kan sayen ƙuri’a

Zaɓe: EFCC ta cika hannu da mutum 12 a Kano da Katsina kan sayen ƙuri’a

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Rasha da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa (EFCC) ta ce, ta tsare mutum 12 bisa zargin sayen ƙuri’a yayin zaɓen cike givin da ya gudana a Kano da Katsina ranar Asabar. Shuguban EFCC na shiyyar Kano, Faruk Dogondaji, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa, an kama waɗanda ake zargin da tsabar kuɗi Naira miliyan 1.5 a jihohin Kano da Katsina. A cewarsa, am damƙe 10 daga cikinsu ne a yankin Ƙaramar Hukumar Doguwa, Jihar Kano, sannan biyu a yankin Ƙaramar Hukumar Kankiya a Jihar Katsina. Jami’in ya ce an…
Read More
Zaɓen cike giɓi: NNPP ta lallasa APC a Fagge

Zaɓen cike giɓi: NNPP ta lallasa APC a Fagge

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Jam'iyyar NNPP, Barista MB. Shehu, ya lashe zaɓen ɗan Majalisar Wakilai na ƙaramar hukumar Fagge a Jihar Kano. Nasarar da MB Shehu ya samu ta kawo ƙarshen ɗan majalisa mai wakiltar shiyyar a Majalisar Wakilai, Aminu Sulaiman Goro na Jam'iyyar APC wanda ke kan wa'adinsa na uku a Majalisar. Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Baturen zaɓen Ibrahim Tajo Suraj, ya ce MB Shehu ya samu ƙuri'u 19,024 daga jimillar ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da ɗan takarar Jam'iyyar Labour, Shuaibu Abubakar ya rufa masa baya da ƙuri'u 12,789. Sakamakon zaɓen ya nuna Aminu Sulaiman Goro…
Read More
Ado Doguwa ya lashe zaɓen Ɗan Majalisar Wakilai na mazaɓarsu

Ado Doguwa ya lashe zaɓen Ɗan Majalisar Wakilai na mazaɓarsu

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Alhassan Ado Doguwa, ya lashe zaɓen ɗan Majalisar Wakilai na Mazaɓar Tudun Wada/Doguwa a Jihar Kano. Doguwa ya lashe zaɓen ne yayin zaɓen cike giɓi INEC ta gudanar a ranar Asabar. Baturen zaɓen, Farfesa Sani Ibrahim, shi ne ya bayyana sakamakon zaɓen inda ya ce ɗan takarar Jam'iyyar APC, Ado Doguwa, ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 41, 573. Ya ce ɗan takarar Jam'iyyar NNPP, Yushau Salisu ne ya zo na biyu da ƙuri'u 34,831, yayin da ɗan takarar Jam'iyyar PDP ya zo na uku da ƙuri'u 2,111.
Read More
HOTUNA: Yadda CP Gumel da tawagarsa suka yi rangadi yayin zaɓen cike giɓi a Kano

HOTUNA: Yadda CP Gumel da tawagarsa suka yi rangadi yayin zaɓen cike giɓi a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano mai kula da aikin zaɓe, CP Usaini Mohammed Gumel, tare da sauran haɗakar jami'an tsaro da ke jihar Kano yayin da tawagarsu ke rangadin duba wasu ƙananan hukumomi dan tabbatar da an samu kwanciyar hankali yayin gudanar da zaɓen cike giɓi da ya guda ranar Asaba. A cikin tawagar akwai Shugaban DSS, Sibul Difens, Hukukar Kiyaye Haɗurra, Sojoji da sauran hukumomin tsaro. Wuraren da tawagar ta ziyarta sun haɗar da Zangon Marikita a Rimin Kebe a ƙaramar hukumar Ungoggo, sai Kwaciri Gabas Alasawa da ke ƙaramar hukumar Fagge da sauransu.…
Read More