Editor

9513 Posts
INEC ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Adamawa, Yunusa Ari

INEC ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Adamawa, Yunusa Ari

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari. Dakatarwar na da saba da bayyana 'yar takarar Gwamna ta Jam'iyyar APC a jihar, Aisha Dahiru Binani, da Kwamishinan ya yi a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar yayin zaɓen cike giɓin da ya gudana a ranar Asabar a jihar. Cikin wasiƙar da hedikwatar INEC ta fitar a ranar Litinin, hukumar ta umarci Ari da ya yi nesa da ofishin hukumar da ke Yola, babban birnin jihar. Wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata 17 ga Afrilu, 2023, da kuma sa hannu Sakatariyar INEC,…
Read More
Nasiru Idris ya zama Gwamna mai jiran gado a Kebbi

Nasiru Idris ya zama Gwamna mai jiran gado a Kebbi

Ɗan takarar gwamna na Jam'iyyar APC a Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya zama sabon zaɓaɓɓen Gwamnan jihar. A ranar Lahadi INEC ta bayyana Idris a matsayin wanda ya lashen zaɓen gwamnan jihar bayan kammala zaɓen gwamnan jihar a ranar Asabar da ta gabata. Ya lashe zaɓen ne bayan da ya doke abokin hamayyarsa na Jam'iyyar PDP, Maj-Gen. Aminu Bande (mai ritaya).
Read More
Rubutu kan kai saƙo inda ƙafa ko gaɓɓan jikin ba su kai ba – Zarah BB

Rubutu kan kai saƙo inda ƙafa ko gaɓɓan jikin ba su kai ba – Zarah BB

"Marubuci bango ne kuma tubali a cikin al'umma" Daga AISHA ASAS Jihar Sakkwato na ɗaya daga cikin jihohin da ke ɗauke da ƙwararrun marubuta duk da cewa ba kasafai ake sanin su ba, wata qila hakan ba ya rasa nasaba da daidaitacciyar Hausa da suke amfani da ita, wadda ke hana a gane su da Hausa irin ta Sakwatawa, har sai dai idan su ne suka faɗa. A yau shafin adabi ya ɗauko ma ku ɗaya daga cikin jajirtattun marubuta da suka fito daga Birnin Shehu, Fatima Bello Bala, wacce aka fi sani da Zarah BB. Matashiyar marubuciya ce da…
Read More
Bilbis ya zama Sanatan Zamfara ta Tsakiya

Bilbis ya zama Sanatan Zamfara ta Tsakiya

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta bayyana ɗan takarar Sanatan Zamfara ta Tsakiya ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, Ikra Aliyu Bilbis, a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanata a yankin a zaɓen cike giɓin da da ya gudana Asabar da ta gabata. INEC ta ce Bilbis ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu mafiyawan ƙuri'u 102, 866 wanda hakan ya ba shi damar doke abokin hamayyarsa na Jam'iyyar APC, Sanata Kabiru Garba Marafa, wandavya tsira da ƙuri'u 91, 216. Farfesa Kabiru Abdullahi na Jami'ar Tarayya da ke Gusau, shi ne ya kasance Baturen zaɓen da ya bayyana sakamakon zaɓen.
Read More
Dandalin shawara: Shekara tara da aure, mijina bai taɓa kusanta ta ta sananniyar hanya ba

Dandalin shawara: Shekara tara da aure, mijina bai taɓa kusanta ta ta sananniyar hanya ba

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Don Allah ki taimaka min da shawara. Ni dai daga ƙauyen……..na aiko da wannan saƙo. Ina da shekara 13 aka yi min aure, kuma ni ban san komai da ake yi da namiji ba. Da ya zo kusanta ta ta farko sai ya yi ta baya. Ban gane ba don na ɗauka haka ake yi. Haka ya yi ta yi har muka yi shekara shida, uwaye na ta ƙorafin ban haihuwa. To sai ya zamana na fara samun matsala a ta kashi na, idan tusa ta zo min nai ƙoƙarin hana…
Read More
ALGON ta gargaɗi kwamitin Abba Gida-gida kan zafafa siyasa a Kano

ALGON ta gargaɗi kwamitin Abba Gida-gida kan zafafa siyasa a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomin Nijeriya (ALGON), reshen Jihar Kano ta bukaci Kwamitin Karɓar Mulki na Jam’iyyar NNPP na jihar da ya daina zafafa siyasa da haifar da tashin hankali ko furta kalaman da ka iya haifar da hargitsi. Shugaban ALGON na jihar, Bappa Muhammad ya yi kiran ne a sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kan zargin karkatar da kuɗaɗen al’umma da kwamitin ke yi wa shugabannin ƙananan hukumomin jihar domin bayar da tallafin ƙarashen zaɓen da ke tafe nan gaba. Haka dai na zuwa be bayan da Kwamitin Karɓar Mulki na Gwamnan Kano mai…
Read More
NUSAID ta tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi 750 da kayan abincin azumi a Kano

NUSAID ta tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi 750 da kayan abincin azumi a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata ƙungiya mai zaman kanta a Jihar Kano mai suna NUSAID tare da haɗin gwiwar Zauren Hadin Kan Malaman Kano a ranar Lahadi ta raba kayan abinci da kuɗi a matsayin tallafin azumi ga mutum 750 a Kano. Mutanen, waɗanda suka haɗa da mata da marayu da sauran masu ƙaramin ƙarfi dai sun rabauta da kayan ne a wani vangare na tallafin da ƙungiyar ta saba bayarwa kowacce shekara a watan azumi. A cewar mai kula da tsare-tsare na ƙungiyar, Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa, sun raba kayan tallafin ne domin su rage raɗaɗin rayuwa ga mabuƙata…
Read More
Matsalolin haƙora da yadda za a magance su

Matsalolin haƙora da yadda za a magance su

Daga AISHA ASAS Ciwon haƙora na ɗaya daga cikin curuta mafi ɗaukar hankalin mai tare da su, kuma ciwon ya zama ruwan dare a tsakanin mutane, wataƙila hakan ba ya rasa alaƙa da rashin sanin hanyoyin da ke iya haddasa matsala a haƙoran namu na daga hanyoyin kula da su. Akwai ɗabi'u da dama da muka maida ba komai ba, amma sukan zama silar kamuwa da wata nau'in cutar haƙora. Darasin namu na wannan sati zai karkata ne kan matsalolin da kuma yadda za a iya magance su, don haka ba za mu samu damar nutsewa cikin bayanin yadda muke…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama a Kaduna

*Gwamna El-Rufai ya yi tir da kisan Sojoji sun ce 'yan bindiga sun halaka mutane da dama tare da jikkata wasu a ƙauyen Runji da ke cikin yankin Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Jihar Kaduna. Bayanan sojojin sun ce an kai harin ne ranar Asabar da daddare. Rahotanni farko da sojojin suka fitar sun nuna an ƙona gidajen da ba a tantace adadinsu ba a ƙauyen. Sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harakokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan, ya fitar ta ce rahoton sojojin ya ce an yi ɗauki ba daɗi tsakanin jami'an tsaro da maharan. Rahoton ya ƙara da cewa,…
Read More