Editor

9513 Posts
Zaɓen Adamawa: IGP ya canja Kwamishinan ‘Yan Sanda mai lura da zaɓen jihar

Zaɓen Adamawa: IGP ya canja Kwamishinan ‘Yan Sanda mai lura da zaɓen jihar

Babban Sufeton 'Yan Sanda (IGP), Usman Baba, ya ba da umarnin janye Kwamishinan 'Yan Sanda mai lura da sha'anin zaɓe a Jihar Adamawa, Mohammed Barde. Manhaja ta gano cewar IGP ya sake ba da umarnin gaggawa a kan Kwamishinan 'Yan Sanda mai kula da Jihar Gombe, CP Etim Equa, ya koma Adamawa da aiki don ci gaba da lura da sha'anin zaɓen gwamnan jihar wanda bai kammala ba. Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Abuja, Kakakin Rundunar 'Yan Sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce IGP na bakin ƙoƙarinsa wajen tabbatar da komai ya gudana cikin nasara. A cewarsa,…
Read More
Saƙo ga Musulmai daga Tiktok

Saƙo ga Musulmai daga Tiktok

Daga FATUHU MUSTAPHA Na yi dogon rubutu na kammala a kan wannan bidiyo, amma sai na neme shi na rasa. Dole sai da na sake komawa tiktok na nemo bidiyo ɗin. Ina ganin wannan bidiyo na kasa yana ishara ne da hadisin da aka ce Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) ya faɗa ne, da yake cewa "…Dan Allah ku kula da mata". A fahimtata ya danka su amana ne a hannunmu, amma ko shakka babu, wannan amana ta mata da 'ya'ya da aka damƙa mana, ta tabbata da yawa daga cikinmu mun ci wannan amana. Da farko dai, a…
Read More
Goman Ƙarshe: Da gaske mata addu’ar neman miji suke yi a tahajjud? (I)

Goman Ƙarshe: Da gaske mata addu’ar neman miji suke yi a tahajjud? (I)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Fauziyya da Samira (ba sunan su na gaskiya kenan ba) ’yan uwan juna ne, uwa ɗaya uba ɗaya, tazarar da ke tsakanin su ba ta wuce ta shekaru 2 ba, aƙalla za su kai shekaru 30 zuwa 35. Suna zaune ne a wani babban gari dake arewacin Nijeriya. Mahaifin su Alhaji Usman (ba sunan ainihi ba ne) dattijo ne mai rufin asiri daidai gwargwado. Babu abin da ya fi ƙaunar gani a duniya kafin Allah ya ɗauki ransa kamar ya ga auren waɗannan ’ya’ya na sa mata, waɗanda ya bai wa tarbiyya daidai gwargwado, kuma suke…
Read More
Shugabancin Adamawa: Fintiri ya zarce

Shugabancin Adamawa: Fintiri ya zarce

Hukumar Zaɓe ta bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Jihar Adamawa. Sakamakon zaɓe ya nuna Fintiri ya lashe zaɓen cike giɓin da ya gudana a jihar Asabar da ta gabata da ƙuri'u 9,337 wanda hakan ya ba shi damar doke abokiyar hamayyarsa ta Jam'iyyar APC, Sanata Aishatu ‘Binani’ Dahiru wadda ta tsira da ƙuri'u 6,513. Bayan kammala zaɓen baki ɗaya, alƙaluma sun nuna Fintiri ya tashi da ƙuri'u 430,861, yayin da Binani ta samu ƙuri'u 398,788. Da yammacin ranar Talata INEC ta kawo ƙarshen tirka-tirkar zaɓen na gwamnan Adamamwa inda ta…
Read More
INEC ta tsayar da ranar bayyana sakamakon zaɓen Gwamnan Adamawa

INEC ta tsayar da ranar bayyana sakamakon zaɓen Gwamnan Adamawa

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta tsayar da ranar da za ta bayyana sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa. Ya zuwa ranar Alhamis ake sa ran INEC ta bayya sakamakon zaɓen na Adamawa. A cewar Kwamishina a hukumar, Dr Festus Okoye, INEC za ta yi zama a ranakun Talata da Laraba don tattauna batun. A ranar Litinin INEC ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa (REC), Hudu Yunusa Ari, saboda riga-malam-masallacin da ya yi wajen karɓe ikon Baturen Zaɓe tare da bayyana 'yar takarar Jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani, a matsayin wadda ta lashe zaɓe tun kafin kammala tattara…
Read More
Sanata Marafa ya amince da shan kaye, ya ce babu batun zuwa kotu

Sanata Marafa ya amince da shan kaye, ya ce babu batun zuwa kotu

Ɗan takarar Sanatan Zamfara ta Tsakiya ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ya amince ya sha kaye a hannun takwaransa na PDP, Hon. Ikira Aliyu Bilbis. A jawabinsa da aka yaɗa ranar Litinin, Marafa ya yi alƙawarin ba zai tafi kotu don ƙalubalantar sakamakon zaɓen ba. Saboda a cewarsa, zuwa kotu zai karkatar da hankalin zaɓaɓɓen sanatan daga barin yin aikin da ya kamata, wanda hakan kuwa zai shafi shiyyarsu. Ɗan siyasar ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa al'ummar Zamfara ta Tsakiya dangane da damar da suka ba shi ta zame musu wakili a…
Read More
An cafke matashin da ya yi garkuwa da ɗan shekara 3 ya binne shi da ransa a Katsina

An cafke matashin da ya yi garkuwa da ɗan shekara 3 ya binne shi da ransa a Katsina

Daga BASHIR ISAH 'Yan sanda a Jihar Katsina sun cafke matashin da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro ɗan shekara uku tare da binne yaron da ransa. Mai garkuwar ya kashe yaron ne bayan kuma ya karɓi fansar N800,000 daga hannun mahaifin yaron. ‘Yan sandan sun ce an damƙe Abubakar Abdul-Aziz ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe uku na rana. Matashin mazaunin Sabuwar Santa Quarters ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Musawa a jihar. Cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin, Kakakin ‘yan sandan Katsina, Gambo Isah, ya ce wanda ake zargin ya shiga gidan wani mai…
Read More
Sanata Binani ta garzaya kotu neman adalci

Sanata Binani ta garzaya kotu neman adalci

'Yar takarar gwamna ta Jam'iyyar APC a Jihar Adamawa, Sanata Aisha Binani Dahiru, ta garzaya kotu don neman a yi mata adalci a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamna a jihar. Aisha ta tafi Babbar Kotu a Abuja ne inda ta shigar da ƙarar neman kotu ta dakatar da matakin da Hukumar Zaɓe, INEC, ta ɗauka na soke bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa bayan zaɓen da ya gudana ranar 18 ga Maris wanda aka kammala ran 15 ga Afrilu. Kazalika, Sanata Binani na neman kotu ta hana INEC ɗaukar wani mataki na gaba dangane da…
Read More
Wanene Jarumi Justus Esiri?

Wanene Jarumi Justus Esiri?

Daga AISHA ASAS Justus Esiri na ɗaya daga cikin tushe da asalin masana'antar finafinai ta Nollywood, kasancewar sa ɗaya daga cikin waɗanda suka fara yin fim tun kafin ta amshi sunanta na Nollywood a shekarar 1960, inda ya soma da wasan kwaikwayo ta gidan talabijin na NTA, wato Nigerian Television Authority, inda ya fara da wani shiri mai dogon zango da aka yi wa suna da 'The Village Headmaster', wanda kusan za a iya cewa ya zama silar shuhurar sa. Justus Esiri ɗan asalin Jihar Delta ne a Oria-Abraka. An haife shi a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 1942.…
Read More
Kotu ta sake aike wa Rarara sammaci

Kotu ta sake aike wa Rarara sammaci

Daga AISHA ASAS Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci a Kano ta bada umarnin sake rubuta wa mawaƙi Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara wata takardar sammaci sakamakon ƙin halartar zamanta da ya yi. Kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito, Kotun wacce ke zamanta a unguwar Rijiyar Zaki da ke birnin Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ta bayar da umarnin yayin zamanta na ranar Talata. Kamar yadda aka faɗa, ana ƙarar mawaƙin ne kan taurin bashin wasu wayoyin da yake karva, yana rabawa mutane daga wurin wani ɗan kasuwa da ake cewa, Muhammad Ma’aji. Kuɗin wanda…
Read More