Editor

9513 Posts
Har yanzu babu jikan Shata da ya nuna sha’awar ya gaje shi – Yalwan Shata

Har yanzu babu jikan Shata da ya nuna sha’awar ya gaje shi – Yalwan Shata

“Mutuwar aure barkatai na damu na” Daga IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD  Hajiya Fatima Yalwan Shata ta na ɗaya daga cikin matan mashahurin mawaƙin Ƙasar Hausa, Marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina. Ta tattauna da Wakilin Blueprint Manhaja, IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD, inda ta yi ma na bayani game da rayuwarta da ta al’umma, har ma da batun siyasa da kuma zamantakewa, wacce kuma ta taɓo batu dangane da yawar mutuwar aure barkatai a Arewa, ta kuma ba da mafita. Ga yadda tattaunawar ta kasance: MANHAJA: Ko mene ne sunanki na yanka? YALWAN SHATA: Sunana Hajiya Fatima, amma an fi sani na da suna…
Read More
Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya kafa Kwamitin Karɓar Mulki

Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya kafa Kwamitin Karɓar Mulki

Gwamna mai jiran gado a Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kafa kwamiti mai mutane 60 a yayin da yake shirin karɓar mulkin ji har. Ofishin zaɓaɓɓen gwamnan ne ya bayyana hakan, a wata sanarwa da Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa Kwamitin yana da alhakin tuntuɓar gwamnatin Gwamna Bello Matawalle mai barin gado, gabanin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu a jihar. Tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, MD Abubakar CFR ne zai jagoranci kwamitin, a yayin da Dr. Hamza Mohammed zai zama Sakatare. Har ila yau,…
Read More
Bikin Sallah: Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutu

Bikin Sallah: Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutu

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranakun Juma'a da Litinin masu zuwa a matsayin ranakun hutun gama-gari albarkacin bikin Idil Fiɗir (Ƙaramar Sallah). Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ta bakin Babban Sakataren Ma'aikatar, Dr Shuaib Belgore. Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya al'ummar Muslimi murnar kammala azumin Ramadan cikin nasara. Haka nan, ya yi kira ga ɗaukacin Muslimi da su yi koyi da kyawawan halayen da Annabi Muhammad (SAW) ya koyar a halin rayuwarsa. Daga nan, Aregbesola ya…
Read More
Jami’ar Ladoke ta haramta wa ɗalibai zuwa makaranta da motocinsu

Jami’ar Ladoke ta haramta wa ɗalibai zuwa makaranta da motocinsu

Daga BASHIR ISAH Hukumar Jami'ar Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ogbomoso ta haramta wa ɗalibai tuƙa motoci a cikin jami'ar da kuma shiga harabarta da motocin kansu. Rijistaran jami'ar, Dr. K.A. Ogunleye, ya ce hukumar jami'ar ta cimma wannan matsaya ne yayin taron da ta gudanar ranar Laraba, 22 ga Maris, 2023. Sanarwar da Hukumar Jami'ar ta fitar ta ce, “Daga yanzu an haramta wa ɗalibai shiga jami'ar da motocin kansu." “Haka nan, ta haramta wa motocin da ba su da lambar rijista shiga jami'ar. Sai kuma batun ajiye motoci ba a bisa ƙa'ida ba a harabar jami'ar wanda hukumar…
Read More
Gwamnati ta umarci Shugaban Hukumar Imigireshan, Isah Idris ya yi ritaya

Gwamnati ta umarci Shugaban Hukumar Imigireshan, Isah Idris ya yi ritaya

Kwamitin Gudanarwa na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya, ya umarci Shugaban riƙo na Hukumar, Isah Idris, da ya gaggauta yin ritaya daga aiki ya zuwa 24 ga Afrilun 2023, ko kuma kafin wannan rana. Sanarwar da Kwamitin ya fitar wadda jaridar News Point Nigeria ta samu leƙawa, ta nuna ƙarewar wa'adin shekara ɗaya da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa Idris a bakin aiki. Kwamitin ya umarci CGI Isah Idris da ya yi murabus kana ya miƙa ragamar jagorancin hukumar ga Mataimakin Kwanturola Janar mafi daɗewa a aiki. Sanarwar mai ɗauke da kwanan wata 17 ga…
Read More
Masu garkuwa sun sace tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi, Okey Wali

Masu garkuwa sun sace tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi, Okey Wali

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), Okey Wali, a Jihar Ribas. Manhaja ta kalato an yi garkuwa da Wali ne biyo bayan harin da aka kai wa tawagarsa da safiyar Litinin a yankin Ƙaramar Hukumar Obio/Akpor a jihar. Kakakin 'yan sandan Ribas, Grace Iringe-Koko, ita ce ta tabbatar da faruwar hakan. Jami'ar ta ce 'yan sanda na bakin ƙoƙarinsu don kuɓutar da Wali cikin ƙoshin lafiya. Ta ce, “Muna sane da batun. Ya faru ne a kusa da yankin Obiri Ikwerre. Muna bincike don tabbatar…
Read More
Dandalin WhatsApp ya raba kayan abinci na sama da Naira miliyan 5 ga mabuƙata a Katsina

Dandalin WhatsApp ya raba kayan abinci na sama da Naira miliyan 5 ga mabuƙata a Katsina

Wata gidauniya da ke ƙarƙashin wani Zauren WhatsApp mai suna Katsina City News, ta tara kuɗi har Naira miliyan biyar da dubu ɗari ɗaya da sha bakwai, inda inda ta riƙa taimakon mabuƙata a lokacin Azumin watan Ramadan. Zauren na WhatsApp wanda na 'yan Jihar Katsina da suka fito daga mabambantan jam'iyyun siyasa da ra'ayoyi daban-daban, sun haɗu ƙarƙashin inuwa ɗaya domin ci gaban Jihar Katsina. Kwamitin Azumi da Zauren ya kafa ƙarƙashin shugabancin tsohon Shugaban Ma'aikata na Jihar Katsina, Alhaji Lawal Aliyu Daura mni, yana da membobi da suka haɗa da Hajiya Mariya Abdullahi Bakori, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina,…
Read More
Dangane da janye dokar hana amfani da tsofaffin kuɗi

Dangane da janye dokar hana amfani da tsofaffin kuɗi

Daga HAFIZ KOZA ADAMU Na fahimci yanzu sababbin takardun kuɗi suna ƙaranci saboda yawaitar tsofaffin takardun kuɗin. A nan sai tunanina ya ba ni to ko masu tsofaffin ne ke fito da ajiyayyun kuɗaɗensu, suna amsar sababbin suna sauyawa, sai kuma sababbin suna sake mai da su ma'ajiya tun da har yanzu ana kan dokar cewa, zuwa Disambar bana za a daina hada-hada da tsofaffin? Idan kuwa haka ne, rufa ta yi, ba ta mutu ba! Na fahimci bankuna ba su cika samun masu shigar da kuɗaɗe ba, mafi akasarin masu zuwa banki ko dai wata matsala ce ta kai…
Read More
Zubar da jini a Arewa: Ya kamata mu farka!

Zubar da jini a Arewa: Ya kamata mu farka!

Daga SHAFI'U DAUDA GIWA Abinda ya ke faruwa a kasar nan har wasu su ke daukarsa tamkar wasa, ko abin nishaɗin da za a zauna a bakin layi a tattauna cikin raha, ko da rabin kwatankwacinsa ya ke faruwa a wata ƙasar wacce ke da cikakkun mutane masu hankali da sanin ciwon kai, da wuya su yarda a kai wani lokaci ba su sauke duk wani shugaba da ke da hannu ko sakaci a cikin abin ba. A yanzu haka mutanen da ke kallon labaran halin da muke ciki suna nan suna mamakin ko mu waɗanne irin mutane ne? Ta…
Read More
Ƙaramar Sallah: Sarkin Musulmi ya buƙaci a nemi jinjirin watan Shawwal ranar Alhamis

Ƙaramar Sallah: Sarkin Musulmi ya buƙaci a nemi jinjirin watan Shawwal ranar Alhamis

Majalisar Ƙoli Kan Harkokin Musulunci na Nijeriya (NSCIA) ta yi kira ga al'ummar Musulmin ƙasar nan da su nemi jinjirin watan Shawwal na shekarar 1444 A.H ranar Alhamis, 29 ga Ramadan 1444 A.H daidai da 20 ga Afrilu, 2023. NSCIA ta buƙaci Musulmi su nemi watan da zarar rana ta faɗi a wannan rana. Wannan kira na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan Gudanarwa na NSCIA, Zubairu Haruna Usman-Ugwu, ya fitar a ranar Talata. Sanarwar ta ce Shugaban NSCIA kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ne ya yi wannan kira bisa shawarar Kwamitin Duban Wata na Ƙasa (NMSC). Sanarwar…
Read More