16
Apr
Daga RABI'U SANUSI a Kano A ranar Asabar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta sake zaɓe a wasu ƙannan hukumomi guda 16 a Jihar Kano. Ƙananan hukumomin Fagge da Ungoggo da Dawakin Tofa da Makoɗa, Warawa da sauran na daga cikin wuraren da sake zaɓe ya shafa. Mahaja ta kalato cewar tun da misalin ƙarfe 7:30 na safe da yawan masu zaɓe sun fito domin kaɗa ƙuri'arsu. Sauran yankun da zaɓen ya shafa har da Gabasawa, Gezawa, Tudun Wada, Doguwa, Gwarzo, Takai, Garko, Wudil, Ajingi, Danbatta da kuma Gaya. Wasu masu sanya ido kan zaɓe sun bayyana wa Manhaja gamsuwarsa…
