15
Apr
Daga AMINA YUSUFU ALI A halin yanzu Babban Bankin Nijeriya, CBN ya shirya tsaf don ganin ya rufe asususn bankunan da ba a haɗa musu BVN a jikinsu ba. Wannan wani mataki ne da suka ɗauka don ganin an rage zambar intanet a bankuna. Blaise Ijebor, Daraktan sashen kula da tsautsayi na CBN shi ya yi yi wannan sanarwar a taron shan ruwa da aka gabatar a ranar alhamis ɗin da ta gabata. Ijebor ya bayyana cewa, mazambatan intanet suna amfani da hanyoyi da dama wajen damfarar asusun da ba haɗa shi da BVN ba. Wanda yake sauƙaƙa musu zambar…
