Editor

9513 Posts
Duk da wadatar takardun Naira masu POS na cajin wuce hankali

Duk da wadatar takardun Naira masu POS na cajin wuce hankali

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu masu sana'ar POS su na cigaba da cajin abokan cinki fiye da kima duk da wadatar takardun Naira a Nijeriya. An gano cewa wasu masu POS a Babban Birnin Tarayya, FCT, na caji tsakanin Naira 300 zuwa N200 kan Naira 5,000 da aka cire. Romanus Chukwu, wani abokin ciniki da aka gani a ɗaya daga cikin wuraren da ke Nyanya, ya ce, har yanzu cajin yana da yawa idan aka kwatanta da lokacin da takardun kuɗi suka yi ƙaranci. Chukwu ya yi kira ga masu sana'ar da su koma karɓar Naira 100 da aka saba…
Read More
Yadda zaɓen cike gurbi na gobe zai iya canja fasalin shugabancin majalisa

Yadda zaɓen cike gurbi na gobe zai iya canja fasalin shugabancin majalisa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gabanin sake zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a gobe, 15 ga Afrilu, 2023, jam’iyyun adawa da ’yan takara, a ƙarshen mako, sun ƙara zage damtse don samun galaba a zaɓen da kuma rage ƙarfin jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar Dokokin Ƙasa. Za a cike zaɓen gwamnoni biyu, na sanatoci biyar, na majalisar wakilai 31 da kuma kujeru 57 na jiha. Jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da na 18 ga watan Maris, inda…
Read More
Tuna baya: Sheikh Ja’afar ya cika shekara 16 da rasuwa

Tuna baya: Sheikh Ja’afar ya cika shekara 16 da rasuwa

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A jiya Alhamis, 13 ga Afrilu, 2023, shahararren malamin addinin Islama, Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya cika shekara 16 da rasuwa. Malam Ja’afar, kamar yada wasu ke kiran sa, ya rasu ne sakamakon harbin binidga a masallacinsa dake gadon unguwar Ɗorayi a birnin Kano yayin da ya ke limancin sallar Asuba ta ranar Juma’a, 16 ga Afrilu, 2007. Shafin Wikipedia ya ruwaito cewa, an haifi Malam Ja’afar a ranar 12 ga, Fabrairu, 1960, kuma ya bar duniya 13 ga Afrilu, 2007. Haifaffen garin Daura ne ta Jihar Katsina, amma ya girma a birnin Kano. Ya rasu ne sanadiyar…
Read More
Tinubu a kotu: Atiku ya saba shan kayin zaɓe

Tinubu a kotu: Atiku ya saba shan kayin zaɓe

*Ya roƙi ga ɗan takarar na PDP*Dalilan da suka hana Atiku cin zaɓe, inji Tinubu Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya ce, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a kodayaushe yana shan kayi a yunƙurinsa na neman shugabancin Nijeriya tun shekarar 1993. Don haka sai Tinubu ya roqi Atiku da kada ya kalli rashin nasararsa a zaɓen da ya gabata a matsayin baƙon abu, yana mai cewa, hakan ba zai zama abin al’ajabi ga Jam’iyyar PDP da ɗan takararta idan aka yi la’akari da rikicin da…
Read More
Giɓin zaɓe: Sufeto Janar ya bayar da tabbacin tsaro ga masu zaɓe

Giɓin zaɓe: Sufeto Janar ya bayar da tabbacin tsaro ga masu zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gabanin sake zaɓen da za a yi ranar Asabar a runfunan zaɓe 2,660 a faɗin ƙasar nan, Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Usman Baba ya ba wa masu kaɗa ƙuri’a tabbacin kare lafiyarsu a rumfunan zaɓe. Ya kuma ba da umarnin tura ’yan sanda zuwa ƙananan hukumomi 185 a faɗin jihohi 24 na tarayya inda za a sake gudanar da zaɓen ranar Asabar. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a lokacin zaɓukan 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris ta bayyana wasu zavukan gwamnoni da na majalisun tarayya da na…
Read More
Sojoji sun kashe ’yan bindiga 15 a Zamfara

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 15 a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar sojoji na ‘Operation Hadarin Daji’ ta Jihar Zamfara ta kashe ’yan bindiga 15 da ke ƙarƙashin shugabancin ƙasurgumin ɗan ta'adda, Dankarami. Waɗanda aka kashe ɗin sun haɗa da babban kwamandan Dankarami, wanda aka fi sani da ‘Jarfa’. ’Yan ta’addan da suka yi yunƙurin kai hari a yankin Gidan Danjimma da Kirifada da ke cikin ƙaramar hukumar Birnin-magaji a ranar Larabar da ta gabata, sojojin tare da ’yan banga sun yi nasarar fatattakarsu. Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, majiya ta shaida wa Blueprint Manhaja cewa ’yan bindigar da yawansu su na gudanar da jana’izar mambobinsu…
Read More
Zaɓen cike gurbi: PDP ta koka a Zamfara

Zaɓen cike gurbi: PDP ta koka a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Yayin da zaɓukan da za a sake ke gabatowa, jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta zargi ’yan sandan Nijeriya da yunƙurin musgunawa mambobinta a jihar a yayin zaɓen. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta ce, za a sake gudanar da zaɓen ne a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, kuma za a gudanar da zaɓen ne na kujerar ɗan majalisar dattawan Zamfara ta tsakiya da kuma kujeru biyu na majalisar wakilai. Ofishin yaɗa labarai na Dauda Lawal a ranar Larabar da ta gabata a Gusau ta ce jam’iyyar ta nuna damuwarta game da katsalandan…
Read More
Maitakobi ya ƙaddamar da shirin ‘KarryGo’ don inganta sufuri a Nijeriya

Maitakobi ya ƙaddamar da shirin ‘KarryGo’ don inganta sufuri a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Sufuri (RTEAN), Alhaji (Dr) Musa Mohammed Maitakobi, ya ƙaddamar da wani shiri na rashin kudi mai taken ‘RTEAN KarryGo’ domin tabbatar da tsarin jigilar kaya a Nijeriya. A yayin da ya ke gabatar da shirin a ranar 12 ga Afrilu, 2023, a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua dake Abuja, Maitakobi ya ce, “RTEAN ta shahara wajen ɓullo da shirye-shirye da tsare-tsare masu tasiri ga rayuwar mambobinta da sauran jama’a. Misali, Tsarin Inshorar Hatsari na Matafiya (TAIS), inda duk motar RTEAN ta shiga cikin haɗari za a ba da kulawar gaggawa a matsayin…
Read More
Badaƙalar Dala biliyan 2.4: Majalisa ta gayyaci Ministar Kuɗi da Malami

Badaƙalar Dala biliyan 2.4: Majalisa ta gayyaci Ministar Kuɗi da Malami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamitin Majalisar Wakilai ta Tarayya da ke binciken zargin badaƙalar kuɗin man fetur har Dalar Amurka biliyan 2.3 ya yi sammacin Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed da takwaranta na Shari’a, Abubakar Malami. Kazalika, kwamitin ya buƙaci Sakataren Gwamnatin Tarayya ya bayyana a gabansa a matsayin wani ɓangare na binciken da yake yi. Shugaban kwamitin, Mark Tersee Gbillah, ne ya bayar da umarnin a lokacin zaman da suka yi ranar Talata. Kwamitin yana bincike ne kan zargin harƙallar sayar da ɗanyen mai kimanin ganga miliyan 48 ga ƙasar China da kuɗinsa ya kai…
Read More
Za mu ci gaba da yi wa ’yan ta’adda ruwan wuta — Babban Hafsan Sojojin Ƙasa

Za mu ci gaba da yi wa ’yan ta’adda ruwan wuta — Babban Hafsan Sojojin Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar-Janar Faruq Yahaya ya ce dakarunsa sun shirya tsaf don kawar da dukkanin ‘yan ta’adda da maƙiya ƙasar nan daga doron ƙasa. Janar Yahaya ya bayyana haka ne a ziyarar bikin 'Easter' da ya kai wa dakarun a barikin sojojoji na Maimalari da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. A jawabinsa, wanda kwamandan rundunar a yankin Arewa maso Gabas, Manjo-Janar IS Ali ya karanta, ya yaba da rawar da dakarun ke takawa wajen murƙushe ’yan ta’adda tare da wargaza maɓoyarsu a duk yankin da ma Yankin Tafkin Chadi.…
Read More