Editor

9513 Posts
Ɗangote ya ƙara wa Nijeriya matsayi da ƙima a duniya – Buhari

Ɗangote ya ƙara wa Nijeriya matsayi da ƙima a duniya – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya yaba wa fitaccen ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Aliko Ɗangote, yayin da yake murnar cika shekaru 66 da haihuwa, tare da yi masa fatan Allah ya ƙaro tsawon rai, lafiya da kuma shekaru masu albarka. Shugaba Buhari ya yaba masa bisa ɗimbin ƙoƙarin da yake yi domin ci gaban ƙasa. Shugaban ƙasar a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu ya fitar, an ruwaito cewa, “Ina taya fitaccen ɗan kasuwa…
Read More
Jihar Kaduna ta buƙaci a ƙara mata kujerun aikin Hajjin 2023

Jihar Kaduna ta buƙaci a ƙara mata kujerun aikin Hajjin 2023

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A daidai lokacin da ake ci gaba da kokawa a kan tsadar kuɗin kujerar Aikin Hajji, Jihar Kaduna, wacce aka ba kujeru mafi yawa a bana, ta buƙaci a ƙara mata guda 500. Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar, Dokta Yusuf Yakubu Alrigasiyyu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kaduna, ranar Talata. Ya ce sun aike da buƙatar ce saboda su ba ɗimbin mutanen da suke son biyan kuɗaɗensu a jihar yin hakan. Idan za a iya tunawa, Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ware wa jihar kujeru…
Read More
Yaɗa ilimin Musulunci ne babban aikin da ke gaban musulmin duniya —Buhari

Yaɗa ilimin Musulunci ne babban aikin da ke gaban musulmin duniya —Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce babban aikin da ke gaban Musulmi yanzu a duniya shi ne yadda za su yaɗa ilimin addinin na haƙiƙa. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a birnin Madina na ƙasar Saudiyya, bayan kammala zagaya Cibiyar Bajekolin Kayan Tarihin Annabi Muhammad (SAW) a birnin, a wani ɓangare na ziyarar aikin da ya kai ƙasar. Ya kuma yaba wa qasar ta Saudiyya kan yadda ta samar da sabbin fasahohi na zamani da za su taimaka matuqa wajen yaɗa koyarwar addinin. Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da…
Read More
Ina raye ban mutu ba, inji Jarumi Al-Amin Ciroma, Baban Lukman

Ina raye ban mutu ba, inji Jarumi Al-Amin Ciroma, Baban Lukman

Daga BASHIR ISAH Da SANI AHMAD GIWA a Abuja Fitaccen ɗan jaridar nan kuma jarumin Kannywood, har wa yau Kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Al-Amin Ciroma, wanda mutane suka fi sani da Baban Lukman na cikin shirin fim ɗin nan mai dogon zango, 'Labarina', ya bayyana cewa, yana nan da ransa, bai mutu ba saɓanin wata sanarwar mutuwarsa da aka yaɗa. Ciroma ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyo mai tsawon daƙiƙa 46 da ya yi aka kuma yaɗa a soshiyal midiya da yammacin ranar Alhamis bayan da labarin ‘mutuwarsa’ ya karaɗe kafafen sada zumunta,…
Read More
An yi jana’izar Ci-garin Katsina

An yi jana’izar Ci-garin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina An yi jana'izar ɗaya daga cikin masu riƙe da sarautar gargajiya a Masarautar Katsina, wato Alhaji Aminu Mamman Dee, mai riƙe da sarautar Ci-gari a masarautar. Marigayin babban aminin Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ne. Tun farko an sanar da rasuwarsa da yammacin ranar Laraba, bayan fama da rashin lafiya, inda ya rasu a cibiyar kula da lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Jihar Katsina. A ranar Alhamis da misalin ƙarfe 10 na safe aka yi jana'izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, a fadar Mai Martaba Sarkin Katsina da ke…
Read More
An yi wa Kakakin ‘Yan Sanda na Katsina da wasu ƙarin girma

An yi wa Kakakin ‘Yan Sanda na Katsina da wasu ƙarin girma

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'Yan Sanda ta Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Babban Sufeton 'Yan Sanda, Usman Baba Alƙali, ta ƙara wa wasu jami'anta shida girma a Katsina ciki har da Kakakin rundunar na jihar, Gambo Isa. Ƙarin girman ya haɗa da wasu jami'ai uku da aka ɗaga darajarsu daga muƙaman Sufurtandan 'Yan Sanda (CP) zuwa Babban Sufurtandan 'Yan Sanda ( CSP). Sauran da lamarin ya shafa su ne, Aliyu Sale, Iliyasu Usman Bugaje da kuma Peter Daniel. An gudanar da bikin ƙarin girman ne a ofishin 'yan sanda da ke Kangiwa Road, G.R.A, Katsina. Haka zalika, manyan jami'an rundunar…
Read More
Tinubu, sarkin nasara!

Tinubu, sarkin nasara!

Daga NASIR I. MAHUTA Tunda Tinubu ya tsaya takara, ban tava kawowa akwai abinda zI iya hana shi nasara ba. Tun kafin 2015 na jima da karantar ɗabi'ar Tinubu, a taƙaice, Tinubu na daga cikin mutanen da nake koyi da su wajen samun nasara a duk abin da zan nema. Tinubu na da wata ɗabi'a da ya sa zai yi wuya ya nemi abu bai samu ba. Allah ne ke ba da nasara, amma akwai ɗabi'a da idan mutum na da ita Allah yana ba shi nasarar a duk abin da ya ke nema. Na san mai karatu zai so…
Read More
Maraba da rusau a Kano, amma fa…..

Maraba da rusau a Kano, amma fa…..

Daga FATUHU MUSTAFA Gaskiya ina murna da wannan mataki da sabon gwamna mai jiran gado ya ɗauka, inda ya yi kashedi ga dukkan waɗanda suka samu filaye a makarantun gwamnati, maƙabartu da masallatai da cewa, gara ma kar su ƙarawa kansu asara, domin yana hawa zai rusa dukkan irin waɗannan gine-gine. To amma fa, bayan dara, akwai wata cacar. A Kano dai an jima ana ruwa, ƙasa na shanyewa. Dama gwamnonin Kano tun zamanin Rabiu Kwankwaso 1999 - 2023 ta sunnanta wa Kano wannan mummunar aƙida domin dai mun san a zamanin sa aka fara yanka… Kano Polytechnic oldside, wurin…
Read More
Hausawa mazauna jihohin kudu: Gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah

Hausawa mazauna jihohin kudu: Gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah

Daga RAHMA ABDULMAJID Abubuwa uku ne ɗauke a cikin wannan gajeren bayanin nawa: Inyamurai na samun tsangwama a jahar Legas tun bayan zaɓen shugaban ƙasa na bana da aka yi ranar 25 ga Fabrairu, 2023, amma duk da tsangwamar ba ta kai ga rasa rayuka ba, sun fara gagarumin shiri na mai da kasuwancinsu Kudu maso gabas wato yankunansu. A duk yankunan Kudu idan 'yan Arewa suka samu matsalar tsaro wanda kan janyo asarar rayuka da ɗimbin dukiya sai dai su bar mu da sallallami da ife-ife, amma ba sa iya yin wani babban yunquri na sauya akalar kasuwancinsu zuwa…
Read More
Akwai buƙatar mutane su iya bambance matsalar nakasa da ta aljannu – Fatima Bello

Akwai buƙatar mutane su iya bambance matsalar nakasa da ta aljannu – Fatima Bello

"Iyaye su rage amfani da magungunan gargajiya ga yara masu matsalar nakasa" Daga ABUBAKAR M. TAHEER Fatima Bello matashiya ce da ta ke taimakon yara masu buƙatar ta musamman, inda ta buɗe gidauniyar tallafa musu mai suna Haske Children Foundation. A cikin wannan tattaunawa da wakilin Manhaja, Abubakar M Taheer ya yi da ita, ta nuna takaicin ta kan yadda al'umma suka ɗauki masu bukata ta musamman a matsayin wani abu da ya shafi aljannu, dama wasu batutuwa da ya shafi taimakon masu buƙata ta musamman. A sha karatu lafiya. MANHAJA: DA farko za mu so ki gabatar mana da…
Read More