13
Apr
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Kwanci tashi ba wuya ga mai yawan rai, ga shi yau har azumin watan Ramadan ya kai rabi. Musulmi a ko'ina a faɗin duniya, sun shagaltu da ayyukan ibada da neman ƙarin kusanci ga Allah maɗaukakin sarki, wajen kamewa daga ci da sha da jima'i a lokacin wuni, wato daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana, da kuma yawaita karatun Alƙur'ani Mai Girma da halartar wuraren tafsiri, zikirori da nafilfili a cikin yini da dare. Lallai babu shakka Ramadan wata ne mai tsarki da ɗimbin daraja, kuma lokaci ne na tsarkake zukata, da ƙara samun tsoron Allah.…
