Editor

9513 Posts
Cece-kucen bayan babban zaɓen Nijeriya

Cece-kucen bayan babban zaɓen Nijeriya

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Gaskiyar magana cece-kucen bayan babban zaɓen Najeriya na 2023 ya sha bamban da sauran zaɓuka daga wanda a ka fara a 1999 bayan dogon mulkin soja da ya zo yayin da su ka kifar da gwamnatin marigayi Alhaji Shehu Shagari bayan babban zaɓen 1983. Kafin na tsunduma gadan-dagan cikin rubutu zan ce babban bambancin shi ne na bambancin addini wanda ko haka ne ko ba haka ba ne siyasar Nijeriya ta wannan karo ta ɗauko bambancin addini ta fito da shi fili ya zama cikin abubuwan da a ka yi amfani da su wajen yakin neman…
Read More
Gwagwarmayar neman shugabancin Majalisar Dokokin Nijeriya ya ɗauki salon addini

Gwagwarmayar neman shugabancin Majalisar Dokokin Nijeriya ya ɗauki salon addini

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Daga dukkan alamu addini zai taka muhimmiyar rawa a yunƙurin da ake yi na samar da sababbin shugabannin Majalisar Dokokin Nijeriya, wacce ta ƙunshi Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai. Bayanai sun nuna cewa, wannan ya biyo bayan kasancewar zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Alhaji Kashim Shettima, dukkansu Musulmi ne. Hakan ya sanya wasu ’yan majalisun masu jiran gado ke kurarin cewa, ba za ta saɓu ba a zaɓi Shugaban Majalisar Dattawa Musulmi, har ma wasu ke ganin cewa, hatta Kakakin Majalisar Wakilai shi ma bai dace ya…
Read More
Hukumar Ƙidaya ta fara aika gayyatar horarwa ga ma’aikatanta

Hukumar Ƙidaya ta fara aika gayyatar horarwa ga ma’aikatanta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) ta fara aika saƙon gayyata zuwa ga masu ƙidayar jama'a da masu sa ido don horar da ma'aikatan wucin gadi. Sanarwar hukumar ta ce, "muna farin cikin sanar da duk waɗanda suka yi rajista a manhajar NPC domin gudanar da aikin ƙidayar jama’a na shekarar 2023 cewa, hukumar gudanarwar hukumar ƙidaya ta ƙasa ta fara aikewa da takardar gayyata horo ga ma'aikata da aka amince da su domin horar da matakin ƙaramar hukumar, wanda aka tsara zai fara a ranar 11 ga Afrilu, 2023." Dangane da saƙon da aka aika a…
Read More
Matar hamshaƙin ɗankasuwa, Aminu Ɗantata ta riga mu gidan gaskiya

Matar hamshaƙin ɗankasuwa, Aminu Ɗantata ta riga mu gidan gaskiya

Hamshaƙin ɗan kasuwar nan na garin Kano, wato Alhaji Aminu Ɗantata, ya yi rashin matarsa Hajiya Rabi Aminu Ɗantata wadda aka fi sani da Mama Rabi. Majiyar jaridar News Point Nigeria ta ce, a ranar Asabar Allah Ya yi wa marigayiyar cikawa a wani asibitin ƙasar Saudiyya bayan fama da rashin lafiya. Mama Rabi, wadda ta kasance mata ta biyu ga Aminu Ɗantata, ta bar duniya tana da shekara 70 da ɗoriya. Kuma ta rasu ta bar mijinta da 'ya'ya shida da suka haɗa da Tajjuddeen Ɗantata, Batulu Ɗantata, Hafsa Ɗantata, Jamila Ɗantata da kuma Aliya Ɗantata. Kazalika, ta bar…
Read More
Tsohon Ministan Shari’a, Bola Ajibola ya kwanta dama

Tsohon Ministan Shari’a, Bola Ajibola ya kwanta dama

Tsohon Ministan Shari'a kuma tsohon Babban Lauyan Nijeriya, Bola Ajibola, ya mutu yana da shekara 89. Ajibola, wanda shi ne ya kafa Jami'ar Crescent da ke Abeokuta, ya rasu ne a ranar Asabar bayan fama da rashin lafiya na dogon lokaci. Babban ɗan marigayin, Segun Ajibola, SAN, shi ne ya bayyana rasuwar mahaifin nasa cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun. Sanarwar ta nuna cewar, “Zuciya cike da alheni da godiya ga Allah Maɗaukaki. “Mahaifinmu, Prince Bola Ajibola, ya bar duniya da tsakar dare. Muna fata Allah Ya yi masa rahma da Aljanah Firdaus.”…
Read More
Mahara sun kashe mutum 38, sun jikkata 51 a Binuwai

Mahara sun kashe mutum 38, sun jikkata 51 a Binuwai

Aƙalla mutum 38 sun mutu, sannan 51 sun jikkata biyo bayan harin da makiyaya suka kai a sansanin 'yan gudun hijira da ke Jihar Binuwai. Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne ranar Juma'a a wata makarantar firamaren da aka bai wa 'yan gudun hijirar mafaka a Gundumar Nyiev cikin Ƙaramar Hukumar Guma da misalin ƙarfe 7 na dare. An ce galibin waɗanda harin ya ritsa da su ƙananan yara ne da muma mata. A cewar wani ganau, "Sun shiga yankin ne daga ɓangarori daban-daban, sannan suka shiga kashe mutane a sansanin." Ihembe Tyubee ya ƙara da cewa, "Hatta…
Read More
Mutane da dama sun mutu, da yawa sun jikkata sakamakon rikicin Fulani da Hausawa a Sakkwato

Mutane da dama sun mutu, da yawa sun jikkata sakamakon rikicin Fulani da Hausawa a Sakkwato

An shiga halin ɗar-ɗar a yankin Gwadabawa a Jihar Sakkwato sakamakon ɓarkewar rikici tsakanin Fulani da Hausawa mazauna yankin. Bayanai sun ce rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama haɗi da soja guda. Wani mazaunin yankin, Aminu Gwadabawa, ya faɗa wa kafar VOA Hausa a hirar da ta yi da shi ranar Asabar cewar, "Mazauna yankin na zaune cikin tsoro sakamakon rikincin ya ci ran wani soja. “Ɓangarorin da rikicin ya shafa kowannensu na ɗari-ɗarin fuskantar fansa daga ɗaya ɓangaren." A cewar wani da ya tsallake rijiya da baya a rikicin, "Fulani sun kai wa ɗan uwana hari da…
Read More
Masu garkuwa sun buƙaci a biya su N70m kafin su sako tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa

Masu garkuwa sun buƙaci a biya su N70m kafin su sako tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa

Waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Mataimaki Gwamnan Jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye Wado, sun bauƙaci a biya su Naira miliyan 70 kafin su sako shi. Binciken Manhaja ya gano a ranar Juma'a masu garkuwar suka yi magana da ahalin wanda ke hannunsu don neman kuɗin fansa. Sai dai majiya ta kusa da Wado ta ce 'yan uwansa sun nemi rage a wajen 'yan bindigar kan su biya Naira miliyan biyu don a sake shi. 'Yan uwan nasa sun nuna damuwa saboda a cewarsu, hutun gama-gari da ake yi zai hana zuwa banki don tattaro kuɗin da suke buƙata. “Masu…
Read More
Kisan Ummita:  Ɗan Chana ya kammala kare kansa a gaban kotun Kano

Kisan Ummita:  Ɗan Chana ya kammala kare kansa a gaban kotun Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan ƙasar Sin ɗin nan mai shekaru 47, Mista Frank Geng-Ƙuangrong, wanda ake zargi da kashe budurwarsa ‘yar Nijeriya, Ummukulsum Sani, wadda aka fi sani da Ummita, mai shekaru 22, ya kamala gabatar da shaidun kare kansa a gaban wata Babbar Kotun dake Jihar Kano. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa wanda ake ƙarar da ke zaune a Railway Quarters Kano ana tuhumarsa da aikata laifuka guda ɗaya na kisan kai. A zaman da aka yi ranar Alhamis, Lauyan da ke kare wanda ake ƙara, Muhammad Dan’azumi ya shaida wa kotun cewa…
Read More
Tinubu: Kansilolin APC sun ba Baba-Ahmed awa 48 ya janye kalamansa

Tinubu: Kansilolin APC sun ba Baba-Ahmed awa 48 ya janye kalamansa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gamayyar Kansilolin Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta bai wa mataimakin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed awanni 48 ya janye kalamansa kan batun cewa gwamnati ta dakatar da rantsar da zavavven Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinibu ba a 29 ga Mayun 2023 mai zuwa. Gamayyar Kansilolin na APC sun bayyana cewa za su ɗauki matakin shari'a matuƙar Datti Baba-Ahmed bai fito ya janye kalamansa ba kuma ya nemi yafiyar 'yan Nijeriya. Idan za a iya tunawa, shi ma Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu na Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed ya zargi…
Read More