08
Apr
'Yan bindiga sun sace mutum 60, galibinsu ƙananan yara, a ƙauyukan da ke kan iyakar jihohin Zamfara da Katsina. Manhaja ta kalato cewar waɗanda lamarin ya shafa sun fito ne daga ƙauyukan Kucheri da Wanzamai da kuma Danwuri da ke cikin Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara da garin Yankara a yankin Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina. Lamarin ya auku ne a ranar Juma'a yayin da 'yan bindigar suka fito daga Dajin Sububu a Jihar Zamfara zuwa dajin Birnin-Gwari a Jihar Kaduna. Duk da dai babu wani bayani a hukumance daga 'yan sandan yankin, amma bayanai sun ce 'yan…
