07
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Ɗinkin Duniya UNFPA ya bayyana cewa akwai mata fiye da dubu 800 da ke rayuwa da cutar yoyon fitsari a sassan Nijeriya da kaso mai yawa a Arewacin ƙasar. Shugaban ofishin na UNFPA reshen jihar Adamawa Dr Danladi Idrissa a jawabinsa yayin yaye mata 50 da suka warke daga cutar ta yoyon fitsari ya ce fiye da rabin masu kamuwa da wannan lalurar ta yoyon fitsari na Arewacin ƙasar wanda ke da nasaba da al’adun al’ummar yankin. Dr Idrissa ya bayyana cewa mata 225 cikin 265 da…
