Editor

9513 Posts
Donald Trump ya gurfana gaban kotu, ya musanta zargin da ake yi masa

Donald Trump ya gurfana gaban kotu, ya musanta zargin da ake yi masa

Tsohon Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya musanta zarge-zargen laifuka 34 da ake tuhumar sa da aikatawa, bayan wani bincike da ya gano cewa ya bai wa wata jarumar fina-finan batsa mai suna Stormy Daniels, toshiyar baki. Trump wanda ya miƙa kansa ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Amurka da ke Manhattan, shi ne Shugaban Ƙasar na farko da ya fara fuskantar tuhuma da ta danganci aikata manyan laifuka. Rahotanni na nuni da cewa, Trump ya ba wa jarumar fina-finan batsar kuɗin toshiyar bakin ne a shekarar 2016. Bayan da ya bayyana gaban kotu, tsohon shugaban na Amurka ya wallafa…
Read More
APC a Delta ta musanta korar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa daga jam’iyyar

APC a Delta ta musanta korar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa daga jam’iyyar

Daga WAKILINMU Jam'iyyar APC ta musanta korar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege daga jam'iyyar kamar yadda rahotanni suka nuna. Da fari rahotanni sun nuna yadda APC a Jihar Delta ta kori Omo-Agege daga jam'iyyar cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Maris da kuma sa hannun Shugaban jam'iyyar na jihar, Ulebor Isaac a madadin shugabancin jam'iyyar a jihar. An ce sun ɗauki matakin korar ne bayan da suka zarge shi da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa da sauran laifuka waɗanda ba a bayyana ba. Sai dai kuma, tsagin APC a jihar da ke yin Mataimakin Shugaban…
Read More
Matsayin dakarun MƊD da aka tsinkaya a Edo – Hedikatwar Tsaro

Matsayin dakarun MƊD da aka tsinkaya a Edo – Hedikatwar Tsaro

Daga BASHIR ISAH Babban Ofishin Tsaro na Ƙasa ya buƙaci jama'a kowa ya kwantar da hankalinsa dangane da motoci da dauran kayayyakin Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gani an girke su a Jihar Edo. Wani faifan bidiyo da aka yaɗa kwanan nan ya nuna yadda aka tsinkayi kayayyakin na MƊD a Benin, babban birnin Jihar Edo. Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata mai ɗauke da da hannun Birgediya Janar Tikir Gusai, Ofishin ya ce ƙasar na ba da gudummawar dakaru ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda na baya-bayan nan shi ne Rundunar Tsaro…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka sace ɗalibai 8 a Kaduna

Yadda ‘yan bindiga suka sace ɗalibai 8 a Kaduna

Daga WAKILINMU Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar cewar an sace wasu ɗaliban jihar su takwas tare da wasu mazauna yankin. Gwamnatin ta ce ɗaliban da lamarin ya shafa ba a harabar makaranta aka sace su ba. A ranar Litinin 'yan bindiga suka sace mutum 10 a Sakandaren Gwamnati da ke Awon a yankin Ƙaramar Hukumar Kachia a jihar. Wannan shi ne hari na baya-bayan da 'yan bindiga suka kai a jihar duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar tare da hukumomin tsaro ke yi wajen daƙile matsalar tsaro a faɗin jihar. Gwamnatin jihar ta bakin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin…
Read More
Ana zargin ɗan sanda da yin garkuwa da jariri ɗan sa’o’i 6 a Legas

Ana zargin ɗan sanda da yin garkuwa da jariri ɗan sa’o’i 6 a Legas

Daga WAKILINMU A yayin da ake ci gaba da gudanar da bikin ranar mata na duniya na shekarar 2023, wata Ƙungiyar Kare Haƙƙin Mata 'Women Advocates Research & Documentation Centre' (WARDC), ta buqaci a yi adalci kan zargin sace wata jariri ɗan kimanin sa'o'i 6 da haihuwa. Ƙungiyar ta kuma yi kira ga babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya da ya gaggauta miƙa ƙarar zuwa hukumar hana safarar mutane ta ƙasa (NAPTIP) a cikin kwanaki 14 ko kuma a kai masa ziyarar zanga-zanga. Baby Joseph, a cewar wanda ta kafa WARDC, Dakta Abiola Akiyode-Afolabi, wadda ta yi magana a…
Read More
Alamomin rushewar zamantakewa

Alamomin rushewar zamantakewa

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a filin zamantakewa na wannan makon. Ya zazumin nan? Fatan Allah ya sa mu yi ibada karɓaɓɓiya. Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan mako muna tafe da alamommin da suke nuna cewa aurenku yana da masassarar mutuwa, wato kwanansa yana gab da ƙarewa. Kamar yadda Hausawa kan ce aure rai ne da shi, duk ranar da wa'adin ajalinsa ya zo, labudda ba ya ƙara kwana, wannan batu haka yake. Idan ajalin aure ya zo, za ka ga alamomi suna ta nunawa. An san dole da ma…
Read More
‘Yan sanda sun ƙaryata shigowar wata baƙuwar halitta cikin Katsina

‘Yan sanda sun ƙaryata shigowar wata baƙuwar halitta cikin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'Yan Sanda a Jihar Katsina ta ƙaryata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo, da ke nuna yadda wata baƙuwar halitta da ba a san ko wacce iri ce ba ta shigo cikin jihar. A cikin sanarwar da Kakakin rundunar, SP Gambo Isa, ya fitar ya bayyana cewa, an jawo hankalin rundunar ‘yan sanda ta jihar kan wani faifan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani da ke nuna yadda wasu baƙin halittu suka mamaye Katsina. “Hukumar tana so ta bayyana cewa abubuwan da ke cikin…
Read More
Tarihin wasu muhimman abubuwan da suka faru a Musulunci cikin watan Ramadan

Tarihin wasu muhimman abubuwan da suka faru a Musulunci cikin watan Ramadan

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ga Musulmin duniya, watan Ramadan, wata ne mai alfarma kuma wanda abubuwa suka faru a cikin watan tarihin Musulunci. Ramadan wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna Ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci. Baya ga kasancewa watan Ibadah, abubuwan tarihi da dama sun faru a cikin Ramadan, wanda shi ne wata na tara a kalandar Musulunci. Jaridar Blueprint Manhaja za ta kawo wasu muhimman abubuwan da suka faru a watan Ramadan, duk da cewa akwai abubuwa da dama na tarihi da suka faru a watan mai alfarma. Saukar da Al-Ƙur'ani: Babban…
Read More
An murkushe baburan ’yan acaɓa 476 da aka kwace a Abuja

An murkushe baburan ’yan acaɓa 476 da aka kwace a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCTA) a ranar Laraba ta ragargaje baburan da ta kwace daga hannun ’yan acaɓa kimanin 476. Hukumar ta kuma sha alwashin ci gaba da nuna ba sani ba sabo a kan tabbatar da bin dokar hana acaɓa a birnin, duk kuwa da irin hare-haren da ta ce ana kai wa jami’anta. Daraktan Sashen da ke Kula da Hanyoyi na hukumar, Abdullateef Bello ne ya sanar da hakan lokacin da ya jagoranci ragargaza baburan a unguwar Area 1 da ke Garki a birnin. Ya kuma lashi takobin cewa za su ci gaba…
Read More
Dole hukumomin tsaro su ja kunnen Datti Baba-Ahmed kan kalaman rantsar da Tinubu – MURIC

Dole hukumomin tsaro su ja kunnen Datti Baba-Ahmed kan kalaman rantsar da Tinubu – MURIC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta yi kira ga hukumomin tsaro su gargadi Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar LP kan cewa kada CJN ya rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu. Farfesa Ishaq Akintola, Babban Direktan MURIC, ya ce akwai ganganci cikin kalaman na Baba-Ahmed. Baba Ahmed ya buƙaci Olukayode Ariwoola, babban alƙalin alƙalan Nijeriya, kada ya rantsar da zavavcen shugaban qasa Bola Tinubu, yana mai cewa hakan saɓa Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ne. Ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tsokaci kan gaza samun ƙuri'u kashi 25 na birnin…
Read More